Rikicin PDP ba don talaka ake yi ba
Daga Basheer Mukhtar Yusuf Zaria Rikicin Jam’’iyyar PDP ba na yi ba ne domin talakan Najeriya, sabuwa da tsohuwar PDP sun shiga akun saka ne domin son biyan bukatun son ransu. Don haka rashin sasantawarsu alheri ne ga talakan Najeriya, musamman idan an yi la’akari da shekaru 14 na dimokuradiyya babu abin da aka tsinana […]
Daga Basheer Mukhtar Yusuf Zaria
Rikicin Jam’’iyyar PDP ba na yi ba ne domin talakan Najeriya, sabuwa da tsohuwar PDP sun shiga akun saka ne domin son biyan bukatun son ransu. Don haka rashin sasantawarsu alheri ne ga talakan Najeriya, musamman idan an yi la’akari da shekaru 14 na dimokuradiyya babu abin da aka tsinana wa talaka, sai tashe-tashen hankula. Yanzu ya rage ga talakawa su yi kokarin sama wa kansu mafita. Idan zabe ya zo, a kauce wa duk wata kumbiya-kumbiya a zabi mutanen da suka dace, amma wadannan mun ga rawarsu. Ta ishe mu haka nan.
Da alamu jam’iyyar PDP ta kama zama hanyar tarihi, tunda ga shi yanzu sai rushe-rushe da kore-kore da sallame-sallamen abokan ci gaba da musguna wa talaka suke ta faman yi, kama daga matakin tarayya zuwa jihohi. Idan mun tuna a makon jiya shugaban kasa ya kori ministan matasa da ci gaban kasa! Kwatsam kuma sai muka sake jin cewa ya kara awon gaba da wasu 9, wai su ma suje gida su huta. Haka sai ya tabbatar mana cewa a kidime yake bai ma san inda hankalinsa yake har yanzu ba. Sannan a Jihar Kaduna, Gwamna Mukhtar Ramalan Yero, ya yi wuju wuju da daukacin majalisar kolin jihar baki dayanta, wanda ya kunshi kwamishinoni kurum, sai kuma Jihar Filato, nan ma Gwamna Jona Jang, ya rusa kwamittin riko ko mu ce kantomomin riko na kananan hukumomin jihar su 17.
Duk wannan rusau da ake ta yi yana zuwa ne a lokacin da bangaren ‘yan tawayen jam’iyyar su Kawu Baraje, ke nan! suke ci gaba da samun karin magoya baya, dan ko a Jihar Kaduna, ai ance ne ana tunani yawancin kwamishinoni da aka rusa suna tare da bangaren su Kawu Baraje ne, Dan haka ya sa ba a yi sanyi waje rusa su ba. Su ba su sani ba!
Hakan na kara karfi ga wancan bangare na tawayen ba ne? Shi kuma bangaren tawayen da jiga-jigansa da ma mun sani ba suna rigima ba domin kwatar wa talaka hakkinsa da ci gaban kasa ba ne, kowa yana yi domin burin kashin kasansa ne. Don haka muna gani su ma din sai sun samu sabani a tsakaninsu. A karshe kurum sai baki daya jam’iyyar duka da daukacin bangarorin biyu su yi su tarwatse, kamar dai fashewar bom. PDP kuma ta zama tarihi. Talakan Najeriya, ya samu ‘yanci. Allah ya tabbatar muna da haka. Amin.
Basheer Mukhtar Yusuf Zaria; 07034514844