Rikicin PDP da APC ya ci samari biyu a Kaduna

Rikicin siyasa da ke ruruwa a tsakanin magoya bayan jam’iyyun PDP da APC ya ci ran samari biyu tare da jikkatar wasu da dama a gwabzawa biyu a Jihar Kaduna.Gwabzawa ta farko an yi ta ne ranar Alhamis din makon jiya a Hayin danmani kusa da Badikko, inda wani matashi dan shekara 20 mai suna […]

Rikicin PDP da APC ya ci samari biyu a Kaduna
Rikicin PDP da APC ya ci samari biyu a Kaduna

Rikicin siyasa da ke ruruwa a tsakanin magoya bayan jam’iyyun PDP da APC ya ci ran samari biyu tare da jikkatar wasu da dama a gwabzawa biyu a Jihar Kaduna.
Gwabzawa ta farko an yi ta ne ranar Alhamis din makon jiya a Hayin danmani kusa da Badikko, inda wani matashi dan shekara 20 mai suna Tijjani Ya’u “Nani” mai sana’ar yin intalok ya rasu bayan an yi masa taron dangi an sare shi a hannu ya yi ta zubar da jini.
Wata majiya ta ce lamarin ya faru ne a lokacin dan takaran Gwamna a Jam’iyyar APC Malam Nasir El-Rufai yake kamfe a garin Rigasa kusa da inda aka gwabza.
Sai da Sanata Sani Sale na Jam’iyyar APC ya ce ba ’yan tawagarsu ba ne suka yi fadar.
Wani ganau Abubakar Sale Badikko ya ce matasan da suka auka wa Badikko sun kai daruruwa dauke da miyagun makamai har suka kone mota Marsandi 190, suka fasa daya suka yi wa wani gida barna.
Malam Abubakar Badikko ya ce marigayin mafarauci ne ba dan banga ba.
An ce ya ki yarda ya karbi tayin da aka yi masa na ya zama cikin samarin da za su yi wa Gwamna rakiya lokacin zabe saboda ya fi son APC. Amma gaba ta mafarauta ta rutsa da shi.
Wata majiya ta ce a ranar Litinin Gwamna Mukhtar Yero ya ziyarci iyalan mamacin da ke Badikko a bayan gidan Gwamna inda ya ya ba su tallafin Naira dubu 100.
Karawa ta biyu ya auku ne yayin da Gwamna Yero ya zo wucewa ta Bakin Ruwa, inda ’yan PDP su ka yi masa lale, amma nan take ’yan APC suka daga hotunan nasu dan takarar.
 Majiyarmu ta ce nan take ’yan sanda da ’yan banga da ke bin Gwamna suka fara harbi da kai farmaki ga mutanen.
Wani da aka sare shi da adda a kafada kuma shugaban ’yan Keke NAPEP da ke kan titin Kagoro daura da Edpress Malam dalhatu Bala ya ce sun fara jin harbe-harbe daga Bakin Ruwa. Sannan motocin PDP uku suka wuce da gilasansu a farfashe, sai ’yan sanda suka fara harbi sannan ’yan banga suka farmaki mutane suka fasa motoci 30 da tayoyin Keke NAPEP da allunan tallar APC.
Wani matashi mai Faisal Umaru Getso da aka harba a wuya da baya da harshashi ya rasu kafin a kai shi asibitin don cire masa.
Mahaifin marigayi Faisal, Alhaji Umaru Getso ya ce “Ina dawowa daga tafiya iyalina suka yi min waya cewa kada in biyo ta Bakin Ruwa domin an fada. Daga baya aka yin min waya cewa an harbe dana, ya cika a hanyar kai shi asibiti.”
Kwamared Shehu Sani ya ziyarci iyalin Alhaji Umaru Getso mahaifin marigayi Faisal wanda ake ganin dan APC ne.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Kaduna SP Aminu Lawan ya ki amsa sakon waya da wakilinmu ya tura masa kan lamarin.