Rikicin PDP: Gwamnoni sun ba Damagum wa’adin yin murabus

An kwashi ’yan kallo a taron gwamnonin PDP kan damabarwar shuagabancin Damagum

Rikicin PDP: Gwamnoni sun ba Damagum wa’adin yin murabus

Gwamnonin PDP sun yi ittifakin cewa Shugaban Riƙo na Jam’iyyar na Ƙasa, Umar Iliya Damagum zai ci gaba da riƙe muƙaminsa har zuwa lokacin babban taron jam’iyyar da ke tafe ranar 24 ga watan nan na Oktoba, 2024.

Hakan na zuwa ne bayan an kwashi ’yan kallo tsakanin gwamnonin Jam’iyyar PDP magoya baya da masu adawa da shugabancin Damagum kafin daga bisani kurar ta lafa.

A zaman da gwamnonin suka yi  ranar Talata ne mai masaukin baƙi, Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Ondo, ya caccaki Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato kan rahsin goyon bayan shugabancin Jam’iyyar ya koma yankin.

Mutfwang daga yankin Arewa ta Tsakiya ya kasance mai adawa da yunkurin tsige Damagum daga shugabancin duk da cewa daga yankin Arewa maso Gabas Damagum yake.

Ana Gwamna Caleb Mutfwang da Ahmadu Fintiri (Adamawa) da Agbu Kefas (Taraba) da Seyi Makinde (Oyo) da kasncewa daga bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, jagoran magoya bayan Damagum.

Aminiya ta gano cewa a taron da gwamnonin suka gudanar ta bidiyo a ranar Litinin, Wike ya bukaci maimakon a tsige Damagun a ba shi damar barin kujerar cikin mutunci, wanda kuma bayan nan ne aka dage taron zuwa Talata domin Damagun ya samu halarta.

Aminiya ta gano cewa bayan tattaunawar ta tsawon sa’o’i a ranar Talata, gwamnonin PDP sun yi ittifakin cewa Damagum zai bar kujerar ne zuwa lokacin babban taron jam’iyyar da ke tafe.

Mun kuma gano cewa a yayin da Damagun zai ci gaba da rike kujewar, taron Kwamitin Zartarwar Jami’iyyar (NEC) da ke tafe zai amince da mayar da shugabancin jam’iyyar yankin Arewa ta Tsakiya tare da sanya ranar babban taron jam’iyyar na kasa.

Bayan sun cimma matsaya ne Mutfwang ya shaida wa Adeleke cewa daga yanzu ya dawo goyon bayan shugabancin jam’iyyar ya koma Arewa ta Tsakiya.

Rabuwar kai ta kunno kai a uwar Jam’iyyar PDP ne bayan rikicin shugabancin da ya haddasa rabuwar kai a Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyar, inda wasu ke neman tsige Damagun.

Rikicin ya kai har ɓangaren jam’iyyar da ke adawa da shuagabancin Damagum na neman ya yi murabus daga kujerarsa, inda har suka naɗa nasu shugaban.

A yayin taron, wanda Damagum da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Shiyyar Kudu, Taofeeq Arapaja, suka halarta, Gwamna Ademola Adeleke, na jihar Ondo, ya bayyana takaicinsa da cewa rikicin na iya sharar zaɓensa da ke tafe a shekarar 2026.

Amma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, Bala Mohammed na Jihar Bauchi, ya ce gwamnonin za su ci gaba da mara wa Damagum baya har zuwa lokacin babban taron jam’iyyar da ke tafe ranar Alhamis 24 ga watan nan na Oktoba.

Ya bayyana wa manema labarai bayan taron gwamnonin a Jihar Ondo cewa sun ba wa Damagum damagar riƙe muƙamin har zuwa lokacin.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara