Rikicin PDP: Haramun ne kwamitin Makarfi ya shirya babban taron jam’iyya – Sheriff

Shugaban bangare na Jam’iyyar PDP ta kasa Sanata Ali Modu Sheriff ya sa kafa ya yi fatali da yunkurin da Kwamitin Dattawan Jam’iyyar yake yi na kawo rikicin jam’iyyar, inda ya ce kwamitin riko a karkashin Sanata Ahmed Makarfi ba ya da ikon da zai shirya babban taron jam’iyyar saboda kwamitin haramtacce ne.Wata sanarwa da […]

Rikicin PDP: Haramun ne kwamitin Makarfi ya shirya babban taron jam’iyya – Sheriff
Rikicin PDP: Haramun ne kwamitin Makarfi ya shirya babban taron jam’iyya – Sheriff

Shugaban bangare na Jam’iyyar PDP ta kasa Sanata Ali Modu Sheriff ya sa kafa ya yi fatali da yunkurin da Kwamitin Dattawan Jam’iyyar yake yi na kawo rikicin jam’iyyar, inda ya ce kwamitin riko a karkashin Sanata Ahmed Makarfi ba ya da ikon da zai shirya babban taron jam’iyyar saboda kwamitin haramtacce ne.
Wata sanarwa da Kakakinsa Mista Inuwa Bwala ya fitar a ranar Talatar da ta gabata, Sanata Ali Sheriff ya soki amincewa da kwamitin Makarfi da kwamitin dattawan jam’iyyar ya yi.
Ya ce, babu wani tanadi a tsarin mulkin jam’iyyar da ya amince da kwamitin riko, kuma kotu ta rika ta bayyana cewa kwamitin haramtacce ne yayin dab ta tabbatar da Sheriff a matsayin shugaban jam’iyyar.
Sanarwar ta kara da cewa: “Bai ma kamata a ambaci kwamitin riko ba a kokarin da ake yi wajen magance rikicin Jam’iyyar PDP ba. Tunfarko ma tilasta kwamitin riko a kan jam’iyyar ne ya jawo tare da ruruta wutar rikicin, kuma duk wani yunkuri da za a yi don halatta ayyukansa, zai dada rura wutar rikicin PDP ne.”
Sanarwar ta kara da cewa: “Wajibi ne wakilan kwamiti dattawan su daina zagaye-zagaye su fuskanci gaskiya wajen amincewa da shugabancin Sheriff har zuwa lokacin da za a shirya babban taron jam’iyyar na gaskiya.”
Sanata Sheriff ya ce Shugaban Kwamitin Dattawan, Sanata Walid Jibrin ya riga ya barar da amanar da galibin wakilan kwamitin suka dora masa saboda rashin tsayawa kan magana daya da neman kudi, don haka ya kauce ya ba mutumin da za a dogara da shi wanda martaba da mutuncinsa ba su girgiza ba, domin jan ragamar Kwamitin Dattawan PDP.
Sanata Sheriff ya ce, kalamai da aikace-aikacen Shugaban Kwamitin Dattawan sun nuna kwamitin ya zama rakumi da akala, inda ya ce, ya jefa martabar babbar jam’iyyar a cikin matsala saboda nuna karkata ga wani bangare da ke takaddamar, maimakon ya zama uba mai sasantawa.
 “Tuni kwamitin sasantawa a karkashin Gwamna Seriake Dickson ya fara gudanar da aikinsa na tattaunawa da bangarorin, sai kwamitin ya bayar da shawarwarinsa kuma Babban Kwamitin Gudanarwa na kasa ya duba kuma ya kira taron Kwamiti Zartarwa don yanke shawara a kai, don haka matakin na kwamitin dattawan bai da wani alfanu,” inji sanarwar.
 Sheriff ya kuma ce wa’adin shugabancin Sanata Walid Jibrin, ya riga ya kare, kuma ya bukaci ya ajiye mukaminsa domin ba da dama a zabi sababbin shugabannin kwamitin.
 A ranar Litinin ce kwamitin dattawan a karkashin Sanata Walid Jibrin ya bukaci kwamitin riko na Sanata Ahmed Makarfi ya kira taron kwamitin zartarwar jam’iyyar na gaggawa kuma ya kafa kwamitin shirya babban taron jam’iyyar na kasa da zai kunshi magoya bayan Sanata Sheriff.