Rikicin PDP: INEC ta amince da dan takaran bangaren Makarfi a zaben Edo
dan takarar Gwamnan Jihar Edo a karkashin Jam’iyyar PDP, bangaren Sanata Ahmed Makarfi, a zaben 10 ga Satumba mai zuwa, Mista Osagie Ize-Iyamu ne Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta amince ya tsaya takara wa jam’iyyar. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce Mataimakin Daraktan Wayar da Kan masu Zabe da Watsa Labarai, Nick […]
dan takarar Gwamnan Jihar Edo a karkashin Jam’iyyar PDP, bangaren Sanata Ahmed Makarfi, a zaben 10 ga Satumba mai zuwa, Mista Osagie Ize-Iyamu ne Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta amince ya tsaya takara wa jam’iyyar. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce Mataimakin Daraktan Wayar da Kan masu Zabe da Watsa Labarai, Nick Dazang ne ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata a Abuja. Mista Dazang ya ce an yanke shawarar amince da Ize-Iyamu ne da Kwamitin Riko na kasa na Jam’iyyar PDP ya gabatar sakamakon hukuncin kotu kan takaddamar PDP.
Ya ce “Hukumar ta karbi takardar fom din dan takarar bangaren Makarfi ne saboda yana da takardar hukuncin kotu da ya ce INEC ta amince da takararsa. Na biyu idan za ku iya tunawa zaben fid da gwani na bangarensa ne kawai hukumar ta sanya ido a kai.” Jam’iyyar PDP ta tsunduma cikin rikicin cikin gida inda bangarori biyu suka da’awar shugabancin jam’iyyar a matakin kasa, kuma bangaren Sanata Ali Modu Sheriff ya gabatar da sunan Matthew Iduoriyekwemwen a matsayin dan takararsa a zaben, bayan bangaren Makarfi ya gabatar da Ize-Iyamu. bangaren Makarfi da ke samun goyon bayan sassan jam’iyyar da suka hada da gwamnoninta da Kwamitin Dattawa ya yi zaben fid da gwani a ranar 20 ga Yuni ne, yayin da na Sheriff ya gudanar da nasa a ranar 29 ga Yuni, sai dai Hukumar INEC ta ce ba za ta amince da kowane dan takara ba, sai kotunan sun yanke hukunci a kan takaddamar. Kotun Tarayya da ke Fatakwal a ranar 4 ga Yuli ta ce babban taron jam’iyyar da aka gudanar day a nada Makarfi shugabancin riko halattaccen ne.