Rikicin PDP: Matasa sun kori shugabanni sun kwace sakatariyarta
APC ke amfani da Sheriff don rusa PDP – Makarfi Laifinku na baya ke binku – APC Jam’iyyar PDP ta sake shiga rudu a shekaranjiya Laraba, bayan da wani da ya nada kansa Shugaban Matasan da suka damu da lamarin PDP (CPDPY) mai suna Aderemi Olusegun ya bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.A […]

APC ke amfani da Sheriff don rusa PDP – Makarfi
Laifinku na baya ke binku – APC
Jam’iyyar PDP ta sake shiga rudu a shekaranjiya Laraba, bayan da wani da ya nada kansa Shugaban Matasan da suka damu da lamarin PDP (CPDPY) mai suna Aderemi Olusegun ya bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.
A ranar Talata Olusegun ya ba shugabannin jam’iyyar na kasa su warware takaddamar sabaninsu ko su dauki mataki, sai dai a shekaranjiya ya mamayi sakatariyar jam’iyyar ya karbe iko da ginin, kuma ya gargadi shugabannin bangarorin jam’iyyar biyu wato Sanata Ali Modu Sheriff da Sanata Ahmed Makarfi da kada su kuskura su kusanci sakatariyar jam’iyyar.
Sakataren Jam’iyyar na kasa Farfesa Wale Oladipo da Oditanta Adewole Adeyanju da suke cikin wadanda taron jam’iyyar na Fatakwal ya rusa, sun shad a kyar daga hannun matasan wadanda suke fusace, bayan da matasan suka iske su a ofisoshinsu.
Wakilinmu ya ce Oladipo yana rokon matasan yana cewa: “Don Allah ku kyale ni in tafi, ba zan sake dawowa ba.”
An fiice da motarsa ta kofar baya da misalin karfe 1:38 na rana kuma mintoci kadan sai aka fice da su daga ginin ta ginin Sky Memorial inda suka tsere daga can.
Bayan ficewar jami’an ne matasan suka bayyana karbe iko da sakatariyar jam’iyyar inda suka bukaci Kwamitin Dattawan Jam’iyyar ya shirya babban taron kasa a cikin kwana uku domin zaben sababbin shugabannin jam’iyyar.
Matasan sun kukkule dukkan kofofin ofisoshin ginin inda suka bayar da mabudansu ga Shugaban Kwamitin Dattawan Sanata Walid Jibrin da misalin karfe 3:30.
Olusegun mai kimanin shekara 30 ya bayyana cewa: “Lura da abubuwan da suke faruwa a PDP, na ayyana kaina a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar. Kuma Sheriff da Makarfi su yi nesa da sakatariyar jam’iyyar tun daga yanzu.”
Sai dai da misalin karfe 5:27, wadansu matasa da suke rera wakokin goyon baya ga Sanata Sheriff sun shiga sakatariyar jam’iyyar bayan sun karya kokfofin shigarta, inda jami’an tsaron sakatariyar suka gaza tabuka komai suka zuba musu ido.
Wannan takaddama tana zuwa ne a lokacin bangaren Sanata Makarfi ya zargi Jam’iyyar APC da rura wutar rikicin da PDP ke ciki domin ta rusa shirinta na lashe zaben shekarar 2019.
Sai dai Jam’iyyar APC ta musanta zargin inda ta ce alhakin abin da PDP ta yi a baya ne yake bin ta. Manyan bangarori biyu na PDP da suke jayayya kan karbe hedkwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, suna karkashin shugabancin tsofaffin gwamnoni ne da kowannensu ya taba zama Sanata sau biyu ko fiye.
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmed Makarfi, wanda aka zaba shugaban riko a babban taron jam’iyyar na Fatakwal, ya karbe iko da sakatariyar jam’iyyar a makon jiya, sai dai a ranar Litinin da ta gabata, tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ya mamayi sakatariyarta da dimbin magoya bayansa, inda ya amshe ta.
An shafe kusan awa bakwai ana kiki-kaka a tsakanin bangarensa da ’yan sanda kafin ya karbe iko da sakatariyar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, inda ya gabatar da umarnin kotu da ya ba shi damar ci gaba da zama shugaban jam’iyyar har zuwa shekarar 2018.
Sai dai a ranar Talata bangaren Sanata Makarfi sun yi zargin cewa Sheriff yana yi wa Jam’iyyar APC aiki ne domin ruguza PDP, domin ta samu nasara a zaben shekarar 2019. Sun yi zargin cewa Sheriff ya karbe iko da Wadata Plaza ne tare da taimakon jami’an Hukumar Tsaron kasa (DSS) da “kuma ’yan bangar siyasa dauke da makamai.”
Kakakin Kwamitin Riko da Makarfi ke jagoranta, Yarima Dayo Adeyeye, ya ce ýkyale Sheriff ya shiga sakatariyar PDP na nuna cewa, Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Solomon Arase ne ya ba jami’ansa suka bude kofarta.
Yarima Adeyeye wanda Sanata Abdul Ahmed Ningi da Sanata Odion Ugbesia da Hajiya A’isha Aliyu suka rufa wa baya, ya yi zargin cewa, gwamnatin APC ta kunyata ’yan Najeriya, don haka jami’anta suke neman hanyar da za su wargaza PDP.
“Jam’iyyar APC ta dauki kwangilar Sheriff da magoya bayansa domin su wargaza damar PDP ta lashe zaben Gwamnan Jihar Edo. Muna da bayanan sirri masu inganci da ke cewa Sheriff ya gana cikin dare a ranar Lahadi da wani Gwamnan APC daga Arewa maso Yamma, inda aka cimma matsaya za a ba shi cikakken tsaro da taimakon kudi ya ruruta wutar rikicin PDP da niyyar a hana mu gabatar da dan takara a zaben Gwamnan Jihar Edo, ko akalla a hana PDP kalubalantar APC, wadda haskenta ke dusashewa a idon masu zabe,” inji Adeyeye.
Sai dai Sakataren Jam’iyyar APC ta kasa, Alhaji Maimala Buni, ya ce munafunci ne PDP ta dora wa APC alhakin halin rudun da ta shiga.
“Ba gaskiya ba ce a ce mun dasa Sheriff a cikin PDP, babu abin da ya hada mu da shi; mu riga mun raba gari tun a wurin babban taronmu kafin zaben bara. barnar da suka tafka a bay ace take bin su, amma suke kokarin huce haushi a kanmu,” inji Maimala.
Alhaji Maimala Buni ya ce APC za ta fi son ta yi muhawara kan abubuwan da za su kawo ci gaban kasa ne maimakon wannan magana marar kan gado da zargin abin dariya.
Ya kara da cewa: “Abu ne sananne cewa PDP c eta jefa kanta a cikin matsala a yau, saboda irin siyasarta ta dauki-dora da sauran halayen da suka saba da dimokuradiyya, wadanda APC take kyama. Don haka PDP ta je ta gyara tsakaninta, maimakon wasa da hankalin jama’a kuma kada su zargi wadansu face kawunansu kan laifuffukan da alhakinsu ke bibiyarsu a yanzu.”
Ya ce a fili yake PDP ta zabi amfani da dabarar kawar da hankali ne saboda gazawarta ta gabatar da dan takarar da ya dace a zaben Gwamna na jihohin Edo da Ondo.
A martanin da Sheriff ya mayar ta hannun kakakinsa, Inuwa Bwala, ya ce mambobin kwamitin riko da Makarfi ke jagoranta ba su da wata madogara, kuma suna ihu ne kawai bayan hari. “A fili yake cewa Sheriff ba ya da ubangida a daukacin harkokin siyasarsa. Ya yi aiki wurjanjan domin zama Gwamnan Jihar Borno sau biyu, ya zama Sanata sau uku, ya kafa tarihi wajen nasarar rayuwar iyalinsa. Zargin cewa APC ce ta daure masa gindi domin ya ruguza PDP, ba gaskiya ba ne, wannan tunani ne na wadanda suke son su yi garkuwa da PDP,” inji shi.