Rikicin PDP: Yadda aka ba hammata iska a Majalisar Tarayya

Ziyarar da shugaban sabuwar PDP Alhaji Abubakar Kawu Baraje ya kai wa Majalisar Tarayya a ranar Talata tare da gwamnoni bakwai, ta tayar da kura har ‘yan Majalisar Wakilai sun ba hammata iska a tsakaninsu.A lokacin dambarwar, wadansu ‘yan majalisa sun yi wa wani dan majalisa Mista Henry Ofonga daga jihar Bayelsa ruwan naushi har […]

Rikicin PDP: Yadda aka ba hammata iska a Majalisar Tarayya

Ziyarar da shugaban sabuwar PDP Alhaji Abubakar Kawu Baraje ya kai wa Majalisar Tarayya a ranar Talata tare da gwamnoni bakwai, ta tayar da kura har ‘yan Majalisar Wakilai sun ba hammata iska a tsakaninsu.
A lokacin dambarwar, wadansu ‘yan majalisa sun yi wa wani dan majalisa Mista Henry Ofonga daga jihar Bayelsa ruwan naushi har suka cire masa riga lokacin da yake nuna adawarsa da ziyarar.
Mafi yawan ‘yan majalisan da suka far wa Ofongo daga jihar Kano suka fito, wadanda suka hada da Aminu Suleiman da Bello Mukhtar da Ali Madaki da kuma Ado Doguwa. Haka kuma Mista Dakuku Peterside da Andrew Uchendu daga jihar Ribas su ma sun tara wa dan majalisar jini a jika domin su hana shi zuwa inda shugabannin majalisa suke zaune.
Ana cikin haka ne sai wadansu ‘yan majalisan da suke goyon bayan Ofongo suka dauko kujera za su yi duka da ita, daya daga cikin wanda ya dauko kujera zai yi duka da ita amma aka rike hannunsa shi ne Mista Ini Udoka daga jihar Akwa Ibom. Shi ma Mista Emmanuel Okon daga jihar Akwa Ibom ya kai wa Ofongo dauki. Udoka da Okon, kamar Ofongo, duk magoya bayan shugabancin Bamanga Tukur ne a majalisar.
Gwamnonin da suka yi wa Baraje rakiya zuwa majalisar su ne: Aliyu Wamako na jihar Sakkwato da Babangida Aliyu na jihar Neja da Rabi’u Kwankwaso na jihar Kano da Rotimi Amaechi na jihar Ribas da Sule Lamido na jihar Jigawa da Murtala Nyaklo na jihar Adamawa da kuma Abdulfatah  Ahmad na jihar Kwara.
Shugaban Majalisar Wakilai, Alhaji Aminu Tambuwal tare da wadansu shugabannin majalisar ne suka karbe su a dakin taro mai lamba 0.28.
Sauran shugabannin majalisar da suke wurin sun hada da Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Mista Emeka Ihedioha da shugabar masu rinjaye Misis Mulikat Akande Adeola da Mai Tsawatarwa a Majalisa, Mista Isiyaka Bawa da Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye, Mista Leo Ogor da kuma Mataimakin Mai Tsawatarwa a majalisa Mukhtar Ahmad.
Bayan an zauna sai aka gabatar da shugaban sabuwar jam’iyyar PDP Kawu Baraje, aka kuma bukaci ya bayyana dalilin zuwansu majalisar, kwasam sai Ofongo tare da Batty Apiafi na jihar Ribas da Bethel Amadi daga jihar Imo da Kingsley Chida daga jihar Ribas da kuma Bitrus Kaze daga jihar Filato suka fado wurin taron, inda Ofongo ya rika fadin akwai gyara!akwai gyara! Ya dumfari inda shugabanni suke zaune domin bayyana korafinsa. Ya ce dole a dakatar da taron domin mafi yawan wadanda suke wurin ba ‘ya’yan jam’iyyar PDP ba ne. Amma sai magoya bayan Baraje suka tare shi, har ta kai ga an fara kai masa naushi, shi kuma Ofongo ya rika mayar da martani da naushi.
A yayin da Baraje ya yi biris da masu korafin ya ci gaba da yin jawabinsa, sai wadansu masu korafin suka kara shigowa suna kururuwa suna fadin kalaman batanci ga sabuwar PDP din, suna cewa, ‘’ ba mu yarda ba sai PDP din Tukur kawai.’’
daya daga cikin masu korafin Apiafi daga Ribas ya yi kukan cewa majalisar tana goyon bayan “abin da ya saba wa doka.’’ Ya fadi a fusace cewa, “wannan saba wa doka ce, PDP daya kawai muke da ita, dole su bar wannan shirmen, don me za mu amince da haka a majalisa? Bai kamata shugaban majalisa ya karbe su ba.’’
Wata ‘yar majalisa wadda ta fito daga jihar Filato,ita ma ta bayyana cewa,’’Tukur ne kawai shugaban PDP da aka sani.’’
Wani dan majalisa daga Kogi ya bayyana ziyarar a matsayin “abin da bai zama dole ba’’ domin hakan zai kara dagula rikicin jam’iyyar ne kawai.
Da ya fito daga wurin da ake taron, Ofongo ya bayyana wa manema labarai cewa, kasancewar dandazon wadanda ba ‘yan PDP ba ne ya ba shi haushi, yana mai nuni da cewa, ‘’Baraje shugaba ne a jam’iyyar, idan ya zo ya ce yana son ya yi mana jawabi babu matsala. Amma sai na ga dandazon wadanda ba ‘yan PDP ba, da na nemi sanin dalili sai suka rika yi mini ihu suka hana ni yin magana.’’
Da yake mayar da martani ga jawabin Baraje, Shugaban Majalisar Wakilai, Aminu Tambuwal ya kauce wa rikicin jam’iyyar PDP din a jawabin nasa, inda a maimakon haka ya ragargaji ‘yan siyasa da laifin yin kokarin wargaza demokaradiyya. Inda ya nuna cewa, son kai maimakon inganta rayuwar mafi yawan jama’a shi ne ya mamaye zukatan ‘yan siyasan.
Ya ci gaba da cewa, abin yana daure masa kai ganin yadda ‘yan siyasa wadanda ba su wuce kashi 25 ba na jama’ar kasar nan suke yi wa masu rinjaye hawan kawara.
Ya ce, ‘’mun damu kawarai da rikita-rikitar siyasar da suke faruwa a kasarmu, musamman a jam’iyyar PDP. Demokaradiyya ta ‘yan Najeriya ce duka ba ‘yan siyasa su kadai ba, mutane da yawa sun rasa rayukansu domin tabbatar da demokaradiyya, shi ya sanya dole ne mu rika gudanar da harkokinmu kamar tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada, kuma mu guji zafafa harkokin siyasa domin cim ma wata bukata ta kashin kanmu.’’
‘Yan majalisan da ke goyon baya bangaren Baraje sun yi wa manema labarai jawabi inda suka la’anci yunkurin da aka yi na wargaza taron. Suna masu nuni da cewa sun je majalisar ne domin su yi wa magoya bayansu bayanin matakin da suka dauka domin yin gyara a jam’iyyar tasu, ‘’amma abin takaici sai wadansu suka zo suka nemi wargaza taron, irin rashin bin dokar da yake faruwa ke nan a jam’iyyar PDP. Abin da muke cewa ba mu amince da shi ba ke nan, duk dai mun ga abin da ya faru.’’
Babu daya daga cikin gwamnonin da ke wurin da ya ce uffan, nan da nan suka shiga motocinsu suka bar wurin.
Shugaban sabuwar PDP din ya kuma kai ziyara ga majalisar dattawa inda ya bayyana musu korafinsu game da shugabancin Bamanga Tukur.
Da yake mayar da martani, shugaban majalisar dattawa Dabid Mark ya tabbatar wa tawagar cewa majalisar za ta dubi korafinsu da idon basira. Tare da bayar da tabbacin cewa majalisar dattawa ba za ta ayyana kujerar kowa a matsayin wanda babu kowa ba saboda wannan dambarwar.