Rikicin Siyasa: ’Yan majalisa 27 sun sauya sheka daga PDP a Ribas
A watan da ya gabata alaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Fubara da uban gidansa, tsohon gwamna Nyesom Wike.
Siyasa a Jihar Ribas ta dauki sabon salo inda 27 daga cikin ’yan majalisar dokokin jihar 32 suka sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.
Enemi George, ya tabbatar da hakan ga manema labarai cewa ’yan majalisar 27 na karkashin jagorancin Martin Amaewhule.
- Malami ya shiga hannun DSS kan yi wa dalibarsa fyade
- Hajji 2024: Kamfanonin jirgin yawo 40 za su yi jigilan maniyyatan Najeriya
Ya ce sun dauki matakin ne a zaman da suka yi da safiyar ranar Litinin.
An shafe makonni ana takun saka tsakanin Amaewhule da wani dan majalisa mai suna Edison Ehie kan rikicin shugabancin majalisar.
Ana kyautata zaton Amaewhule na yin biyayya ga tsohon gwamna Nyesom Wike yayin da shi kuma Ehie yake na hannun dama Gwamna Siminalayi Fubara ne.
Majalisar a karkashin Amaewhule a watan Oktoba ta gabatar da sanarwar tsige gwamnan tare da tsige Ehie a matsayin shugaban majalisar.
Sai dai nan take wasu ’yan majalisar masu biyayya ga Fubara suka tsige Amaewhule tare da nada Ehie a matsayin sabon shugaban majalisar.
Rikicin da ya barke a majalisar mai mambobi 32 ya samo asali ne daga rashin jituwar Fubara da uban gidansa, Wike, wanda yanzu shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya.
Duk da cewa ’yan siyasar biyu sun halarci taro makonnin da suka gabata kuma ga dukkan alamu an samu sasanci.
Amma da ficewar ’yan majalisar 27 daga PDP zuwa APC a ranar Litinin ya bude sabon babi a siyasar jihar.
’Yan SDP Da APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP
A halin da ake ciki kuma, a karshen mako ne wasu ’yan siyasa daga jam’iyyun SDP da APC suka sauya sheka zuwa PDP.
Masu sauya shekar su ne mataimakiyar ’yar takarar gwamna a SDP a zaben 2023, Patricia Ogbonnaya; da tsohon Shugaban Ahoada ta Yamma, Karibo Wilson.
Sun sauya sheka ne tare da magoya bayansu da sauran jiga-jigan jam’iyyar.
’Yan siyasar sun sauya shekar ne don yin biyayya ga Fubara.