Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano

Ana cikin wani yanayi na fargaba a ofishin KNUPDA yayin da duk manyan ma’aikata suka ƙauracewa zuwa aiki.

Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano

Aƙalla wasu mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon ƙazamin rikicin da ya hautsine tsakanin mahukunta da mazauna unguwar Rimin Auzinawa da ke Karamar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.

Bayanai sun ce an harbe mutanen huɗu ne yayin da suka fito tirjiya kan rusau ɗin gine-gine da jami’an hukumar tsara birane ta Jihar Kano KNUPDA suka aiwatar.

Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa galibin gidajen da rusau ɗin ya shafa tuni KNUPDA ta shafa musu alamar cewa aiki zai biyo ta kansu.

Ana dai zargin cewa gine-ginen aƙalla 40 da mahukuntan suka rushe an yi su ne a kan fulotan Jami’ar Bayero da ke Kano.

Sai dai wani mazaunin yankin da ya zanta da Aminiya, ya ce tun da jimawa Hukumar ta KNUPDA ta warware wannan matsala kuma ta jaddada musu cewa a halastaccen matsuguninsu suke domin bai shiga harabar jami’ar ba.

“Mun jima da warware wannan matsala da KNUPDA. Sun tabbatar mana cewa gine-ginenmu ba su shiga harabar jami’ar ta Bayero ba.

“Amma kwatsam sai ranar Lahadi da daddare jami’an KNUPDA suka zo suka yi mana rusau.

“A yayin da wasu daga cikin mazauna suka yi ƙoƙarin tirjiya ne suka harbi mutum huɗu da yanzu an yi musu jana’iza. Wannan abun takaici ne.

Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Manajan Darekta na KNUPDA amma lamarin ya ci tura.

Kazalika, wakilinmu da ya ziyarci ofishin KNUPDA ya tarar da shi fayau a yayin da duk manyan jami’an sun ƙauracewa ofishin domin fargabar kawo musu harin ramuwa kamar yadda wani ƙaramin ma’aikaci ya tabbatar.

“Ana cikin wani yanayi na fargaba a ofishin nan. Shi ya sa ko wurin ajiyar motoci ya zama fayau don duk manyan ma’aikatan babu wanda ya shigo.

“Yanzu haka ƙananan ma’aikata ne kawai suke zaman dabaro a ofishin ba tare da sanin madafar da za a kama ba.

Wani babban Darektan KNUPDA da Aminiya ta tuntuɓa, ya ce ba ma’aikatansu ne suka yi rusau a unguwar ba, inda ya ba da tabbacin cewa jami’ai ne daga Ma’aikatar Ƙasa da Tsara Birane ne suka aiwatar da aikin.

Haka kuma, wani jami’i daga ma’aikatar wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce wuraren da aka yi rusau mallakin Jami’ar Bayero ne kuma nan gaba kaɗan za a fitar da sanarwa a hukumance.

Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke

Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano

Alawar yara mai sanya maye ta shiga gari —NDLEA

NHIS: Kotu ta tsare Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje