Rikicin sarauta: Bwari ta bare
Bayan rasuwar Mai martaba Sarkin Bwari Alhaji Musa Muhammad Ija-Koro a ranar Talatar makon jiya, bangaren masarautar ta Esu Bwari, J.P Ibrahim Yaro, ya sake tayar da dadaddiyar takaddamar da ke tsakaninsu a kan wanda ke da ikon rike masarautar. Aminiya ta ji ta bakin bangarorin biyu da matakan da suke shirin dauka: A ranar […]
Bayan rasuwar Mai martaba Sarkin Bwari Alhaji Musa Muhammad Ija-Koro a ranar Talatar makon jiya, bangaren masarautar ta Esu Bwari, J.P Ibrahim Yaro, ya sake tayar da dadaddiyar takaddamar da ke tsakaninsu a kan wanda ke da ikon rike masarautar. Aminiya ta ji ta bakin bangarorin biyu da matakan da suke shirin dauka:
A ranar Talata 29 ga watan Agusta ne Allah Ya yi wa Mai martaba Sarkin Bwari Alhaji Musa Muhammad Ija-Koro rasuwa yana da shekara 74 bayan jinya ta tsawon shekaru. Sarkin wanda ya shafe shekara 41 yana sarautar kasar Bwari, ya bar mata 4 da ’ya’ya 21 da kuma jikoki 53. An haife shi a ranar 23 ga Mayun 1943 a garin Ija-Koro da ke karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja a lokacin da kimanin kashi 70 cikin 100 na yankin Birnin Tarayya, Abuja ke karkashin masarautar Suleja, kamar yadda Santalin Sarkin Bwari, Alhaji Yunusa Mamman, ya bayyana.
Ya yi karamar firamare ta Bwari a lokacin yana hannun Hakimin Bwari, dan Galadiman Suleja Alhaji Abubakar Barau Musa Angulu, sannan ya wuce babbar firamare ta Suleja sai Sakandaren Bidda sai wata a Zuru, sannan Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ya aiki a matsayin malamin gona a garuruwan Suleja da Bidda da kuma Abuja kafin ya hau sarautar Bwari a 1976, kuma aka ba shi sanda sarauta mai daraja ta biyu a zamanin Ministan Abuja, Janar Jerimiah Useni lokacin mulkin marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha a 1997.
Bayan ba shi sandar girman ce, kabilar Gbagyi wadda ita ce kabila mafi rinjaye a yankin suka nuna rashin amincewarsu da matakin wanda sakamakon haka, gwamnatin ta bai wa masarautarsu sanda mai daraja ta 3 kuma masu sarautar hakimin garin, yayin da shi kuma Sarki ya ci gaba da sarautar kasar Bwari gaba daya da dagatai kamar 10 a karkashinta.
Wasu majiyoyi sun bayyana wa Aminiya cewa sake fasalta tsarin dagatai da ke karkashin masarautar Bwari bayan kafa Abuja inda mafi yawan na farko ’yan kabilar Koro ne da Sarki Ija-Koro ke rike da sarautunsu, sun koma bangaren Jihar Neja, a yayin da sababbi kuma da aka kirkiro kabilar Gbagyi ke da mafi yawan dagatan, kuma sakamakon haka ne sai mafi yawan dagatan masarautar suka maida biyayyarsu ga bangaren Esu, maimakon Sarkin Bwari, sannan ita kanta karamar hukumar wadda ’yan kabilar Gbagyi ne ke shugabancinta suka mayar da Sarkin saniyar ware.
Aminiya ta zanta da Hakimin Bwari wato Esu Bwari Mai girma Ibrahm Yaro kan mene ne matsayar fadarsa a kan takaddamar bayan rasuwar Sarki a yanzu. Esu Bwari wanda shi ne na 17 a bangaren sarautar gidan kuma na 2 bayan ba ta sanda mai daraja ta 3, ya ce fadarsa na kan bakanta ta neman mayar da daukacin sarautar bangarenta. Esun ya ce a daukacin masarautun Abuja, kabilun yankn ne ke jagorantar yankunansu, saboda haka ya ce bangarensa zai yi iya kokarinsa wajen ganin an bai wa kabilar Gbagyi hakkinta.
“Ba ma adawa da bai wa kabilar Koro sarauta a inda suke da rinjaye kamar garin Shere ko Kawu ko Dutsen-Alhaji, amma ba nan Bwari ba. Abin da ya faru an yi shi ne a lokacin mulkin Soja, yanzu kuma zamani ne na dimokuradiyya kuma za mu kai korafinmu gaban Ministan Abuja karkashin wannan gwamnatii na canji don ganin an share mana hawaye. Iyayenmu ne suka kafa garin nan tun a karni na 17 lokacn da farauta ta kawo su nan tare da iyalansu. Shi kansa sunan garin ya samo asali ne daga kalmar “Baya” wato yi daka a nan, amma zuwan Hausawa ne kasancewar sunan ya yi masu nauyi, suke cewa Bwari, sai muka bi su a hakan sunan ya sauya daga kalmar Baya,” inji Esu Bwari.
Ya kara da cewa: “Ko wace karamar hukuma a nan Abuja na da hakimai sama da daya wasu har hudu amma mu a nan Bwari sai a ka bar mu da daya. Sannan irin haka ya faru a garin Kwali inda Sarkin garin wanda daga Masarautar Suleja ne aka nada shi ya rasu, bayan al’ummammu na Gbagyi da ke wajen sun nuna rashin amincewarsu a kan nada wani sabon Sarki, sai gwmanti ta jingi ne sarautar har yanzu ba a sake nada wani Sarki ba.”
A martanin fadar Masarautar Bwari wanda daya daga cikin ’ya’yan marigayi Sarkin Alhaji Abubakar Musa Ija-Koro, Makaman Bwari ya yi bayani a madadinta, ya ce sarautar da mahaifinsu ya rike ta faro ne tun 1902 lokacin da Ma’aji Ali ya rike sarautar sannan wadansu sarakuna biyu suka biyo baya kafin mahaifinsu ya riki sarautar daga 1976 zuwa rasuwarsa.
Makaman ya ce bayan gwamnatin Shugaban kasa Murtala ta kafa Abuja a 1975 ta bai wa daukacin sarakunan Abuja zabin zama a yankin a matsayn sarakuna ko su koma bangaren jihohin da suka fito bayan raba jihohin da Abuja inda za a kafa mUsu sabuwar masarauta, amma sai mahaifinsu ya zabi zama a Abuja, ya ce, ko wadanda suka koma a ka biya su diyya ta hanyar kafa musu sabuwar masarauta.
Makaman na Bwari ya ce lokacin, mahaifnsu wanda ya yi nasarar zama hakimin garin bayan fafatawa da wakilan gundumomi 10 na asalin Bwari da ke da dagatai ’yan kabilar Koro 7 da na Gbagyi 3 a lokacin, sai ya zabi ci gaba da zama a yankin Abuja a yayin da na bangaren Esu kuma sai ya zabi komawa bangaren Neja, inda aka kafa masa gari a waje mai suna New-Bwari (Sabon Bwari) da ke karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja.
“Dalilin hakan an biya Esu na wancan lokacin dukan diyya a yayin da mahaifinmu kuma bai amfana da wata diyya ba. Daga can ne kuma aka dauko Esu na yanzu bayan rasuwar wanda ya gada, saboda haka idan ana bayanin asali shi ma asalinsa Neja ne ke nan kamar ita kanta Abuja. “Kasancewar ba su gamsu da matakin na gwamnati ba, sun kai masarautar nan kara har zuwa Babbar Kotun Abuja, inda kotu ta tabbatar da masarautar nan kafin suka hakura da maganar,” inji Makaman Bwari.
Ya kara da cewa: “Sake tada maganar a yanzu ya ba mu mamaki, kuma muna ganin akwai wani dalili da suke boyewa a kan kiyayyarsu ga wannan masarautar amma ba maganar asali ba. Akwai masarautu da dama a nan Arewa da asalinsu daga Sakkwato ne, misali guda da zan ba ka shi ne masarautar Ilorin wadda Bafulatani ne asalinta maimakon Yarbawa da ke da rinjaye a garin da kuma Jihar Kwara.”
Wata majya mai tushe a masarautar ta tabbatar wa Aminiya cewa, tuni ’ya’yan Sarkin suka hada kansu tare da zabin daya daga cikinsu mai suna Alhaji Auwal Musa Muhammad Ija-Koro wanda shi ne Chiroman Bwari a matsayiin wanda suke so ya gaji kujerar, inda kuma masu zaben Sarki na masaurautar suka amince, kuma ake jiran amincewar Ministan Birnin Tarayya, Malam Muhammad Musa Bello wanda ke da ikon yanke hukunci na karshe.