Rikicin Sarautar Kano: Kotu ta haramta wa lauyoyi hira da ’yan jarida

Babbar Kotun Jihar Kano, ta bai wa lauyoyi umarnin daina da hira da manema labarai kan shari’ar dambarwar Masarautar Kano.

Rikicin Sarautar Kano: Kotu ta haramta wa lauyoyi hira da ’yan jarida

Babbar Kotun Kano ta umarci lauyoyi da su daina yin hira da manema labarai kan dambarwar masarautun jihar.

A zaman kotun na ranar Alhamis ne Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta ba da umarnin.

Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, wadda ke sauraron shari’ar mai sarkakiya ta ce, “Ina umartar ku lauyoyi kada ku yi hira da ’yan jarida kafin ko bayan hukuncin da na yanke kan rokon da wanda ake kara na farko ya gabatar na neman dakatar da wannan shari’a.”

Daga nan ta tafi hutun takaitaccen lokaci domin ta dawo ta sanar da hukuncin da ta yanke kan shari’ar da ke gabanta.

Antoni-Janar na Jihar Kano da Majalisar Dokoki da shugabanta ne suka shigar da kara gaban kotun.

Sun garzaya kotun ne ranar 27 ga watan Mayu 2013, suka nemi ta umarci Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna hudu da aka rushe masarautunsu daga gabatar da kansu a matsayin sarakunan masarautun na Bichi, Gaya, Karaye, da Rano.

Wadanda ake kara su ne Alhaji Aminu Ado-Bayero, Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado-Bayero Bichi, Sarkin Karaye Dr Ibrahim Abubakar ll, Sarkin Rabo Alhaji Kabiru Muhammad-Inuwa, da kuma Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim-Gaya.

Sauran wadanda ake kara su ne Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Daraktan Hukumar Tsaro tacDSSn a Jihar Kano, da Kwamandan Sibil Difens na jihar da kuma Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya.