Rikicin Shugabanci: ADC ta kori Nafiu Bala da wasu 10 daga jam’iyyar
Jam’iyyar ta zargi Nafiu da wasu da ƙoƙarin raba kawunan mambobinta.
Jam’iyyar ADC tsagin David Mark, ta sanar da korar Nafiu Bala Gombe, wanda ke iƙirarin shugabancin jam’iyyar, tare da wasu mutum 10 bisa zargin aikata ayyukan da suka saɓa wa dokokin jam’iyyar.
An ɗauki wannan mataki ne yayin Babban Taron jam’iyyar na Ƙasa karo na takwas da aka gudanar a Abuja ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, 2026.
- Ba sani ba sabo kan yaƙi da rashawa — Kwamishinan ’Yan Sandan Gombe
- Bashin da ake bin Najeriya ya ƙaru da N14.61trn a 2025 — DMO
Mambobin jam’iyyar da suka halarci taron sun amince da korar su ne bayan gabatar da rahoton kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.
Waɗanda aka kora sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Nafiu Bala Gombe, Hon. Leke Abejide: ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Yagba daga Jihar Kogi.
Sauran sun haɗa da Kingsley Temitope, Stella Chukwuma, Odion Kennedy, da wasu mutum huɗu.
Dalilin korar su
Kwamitin ladabtarwa ya bayyana cewa an bai wa mutanen lokaci domin su daina sikata ayyukan da suke yi na neman rarraba kawunan jam’iyyar, amma suka ƙi yin hakan.
Haka kuma, an zarge su da garzayawa kotu ba tare da bin matakan sasanci na cikin gida ba, wanda hakan ya saɓa wa sashe na 92 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Rikicin Shugabanci
A halin yanzu, jam’iyyar ADC tana fama da rikicin shugabanci tsakanin ɓangaren Sanata David Mark, wanda babban taron ya amince da shi, da kuma ɓangaren Nafiu Bala Gombe.
A ranar Talatar dai, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ɗage sauraron shari’ar da Nafiu Bala ya shigar har sai bayan hukuncin kotun ƙoli kan ɗaukaka ƙarar da David Mark ya yi.
Taron na ranar Talata ya kuma sake jaddada goyon baya ga Sanata David Mark a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar na ƙasa na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.