Rikicin shugabanci na kawo tarnaqi ga kungiyar sintiri – ‘Ya’yan kungiya
An yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki mataki ingantacce domin kawo karshen rikicin da ya dabaibaye kungiyar sintiri ta kasa wato Bigilante Group of Nigeria (BGN) domin samun cikakkiyar damar gudanar da ayyukanta na taimaka wa hukumomin tsaro wajen kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma. Wannan roko ya fito ne daga wasu daga […]
An yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki mataki ingantacce domin kawo karshen rikicin da ya dabaibaye kungiyar sintiri ta kasa wato Bigilante Group of Nigeria (BGN) domin samun cikakkiyar damar gudanar da ayyukanta na taimaka wa hukumomin tsaro wajen kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma. |
Wannan roko ya fito ne daga wasu daga cikin ’ya’yan kungiyar da ke Jihar Kano Malam Ado Gona da Haruna gwamnati a zantawarsu da wakilin mu bayan sun kammala aikin tabbatar da tsaro a wasu masallatan juma’a, inda suka sanar da cewa rikicin shugabanci a mataki na kasa da ake yi tsakanin shugaban kungiyar ta BGN Alhaji Ali Sakkwato da kuma bangaren Usman Jahun ya na kawo matsala ga kungiyar kuma akwai bukatar gwamnatin tarayya ta gaggauta shiga tsakani domin ganin an kawar da wannan matsala ta rikicin shugaban ci a kungiyar.
Haka kuma sun nunar da cewa rikicin da ake yi tsakanin Usman Jahun da Ali Sakkwato ya haifar da koma baya a harkokin kungiyar sannan ana samun baraka a wajen ba da umarnin aiki wanda hakan na kawo wa ayyukan kungiyar tarnaki, inda suka bukaci hukumomin tsaro da ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasa da dukkanin masu ruwa da tsaki a fannin tsaro da su taimaka wajen kawo karshen wannan rikici tsakanin babban kwamandan kungiyar wanda aka sani wato Alhaji Ali Sakkwato da kuma Usman Jahun wanda yake ikirarin cewa shi ne kwamanda.
Daga karshe, ’yan bangar sun sanar da cewa a fannin tsaro ana bukatar samun umarni da murya daya, don haka yana da kyau a dubi wannan lamari ta yadda za a sami damar inganta kungiyar musamman ganin cewa akwai mambobin ta a kowane lungu da sako na fadin kasar nan inda suke gudanar da ayyukan tsaro dare da rana tun da aka kafa ta bisa jagorancin mutane masu kishin kasa irin su Alhaji Ali Sakkwato wadanda suka sadaukar da dukiyar su domin tabbatar da kafuwar kungiyar a kasa baki daya.