Rikicin shugabanci ya kunno kai a tsakanin Hausawan Apata
Jayayyar shugabanci a tsakanin al’ummar Hausawa mazauna Apata, kusa da birnin Ibadan, wadda aka fara makonni 5 da suka shige, ta haifar da girke jami’an tsaro domin hana barkewar tarzoma. Dalilin jayayyar ya biyo bayan nadin da fadar Sarkin Hausawan Ibadan ta yi wa Alhaji Sahabi Sulaiman, a matsayin sabon Sarkin Hausawan Apata, wanda shi […]

Jayayyar shugabanci a tsakanin al’ummar Hausawa mazauna Apata, kusa da birnin Ibadan, wadda aka fara makonni 5 da suka shige, ta haifar da girke jami’an tsaro domin hana barkewar tarzoma.
Dalilin jayayyar ya biyo bayan nadin da fadar Sarkin Hausawan Ibadan ta yi wa Alhaji Sahabi Sulaiman, a matsayin sabon Sarkin Hausawan Apata, wanda shi kuma ya ambaci Alhaji Mu’azu Muhammed, a matsayin waki-linsa, wanda wasu ba su yarda da hakan ba.
A cewar masu jayayyar, Malam Juma Abdullahi, babban dan marigayi Sarkin Hausawan Apata, shi suke so ya zama wakili, saboda haka ma suka gudanar da bikin nadin nasa, a boye a unguwar Sabo, kamar yadda wakilinmu ya gano, lamarin da ke nuna samuwar rabuwar kawunan al’umma da kasawar shugabanni wajen yin maganinta.
Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru ya nuna ba shi da masaniya dangane da nadin, amma cikin hirarsu da wakilinmu, ya ce an tabbatar da nada Alhaji Sahabi Sulaiman ne bayan samun goyon bayan mutanen Apata.
Ya ce an dakatar da batun nadin wakili sai nan gaba, a dalilin jayayyar, “Wadda, ina tabbatar maka za mu yi adalci wajen shawo kan matsalar”. Inji shi.
Wakilinmu ya tuntubi Sarkin Hausawan na Apata, Alhaji Sahabi Sulaiman, mai shekaru 75, wanda kuma ya yi shekaru 43 a garin na Apata, sai ya ce yana, “Neman tsarin Allah daga shaidanun da suke kokarin ruruta wuta a maimakon fahimtar juna da zama lafiya a tsakaninmu. Wallahi tallahi mutanen da muke zaune tare da su ne suka tilasta ni karbar mukamin Sarkin Hausawa bayan rasuwar marigayi Malam Audu, kuma mu duka muka amince da nada Alhaji Mu’azu Muhammed, a matsayin wakili, saboda kyawawan halayensa da rike amana da son zama lafiya da ci gaban jama’arsa”.
Alhaji Sahabi, wanda yake tare da ’yan majalisarsa da babban sakatarensa, Alhaji Aliyu Salau Zamfara, ya bayyana cewa sun aika wa Sarkin Hausawan Ibadan takarda, “Har sau 3 a game da wakilin da muke so mu nada kuma jami’an tsaro suna sane da hakan, amma abin mamaki sai muka samu labarin an nado wani a matsayin wakili, bayan wanda muka nada tuntuni. Yin hakan, ya nuna cewa, akwai shaidanun da suke kulle-kullen makirci a baya domin tayar da hankalin jama’a. Saboda haka muka yi maraba da ganin jami’an tsaro da aka girke domin kwantar da hankalin jama’a da zama lafiya, duk dayake tun farko, na ja kunnen jama’a kan zaman lafiya da guje wa yanke wa kansu hukunci”.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sardau-nan Yamma, Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin ya bukaci shugabannin al’umma su tashi tsaye wajen wayar da kan jama’a a game da muhimmancin zama lafiya. “Bai kamata mu kyale mutane kara zube ba tare da alkibla ba, domin ci gaba da aukuwar wannan al’amari a tsakanin Hausawan Apata, babbar illa ce gare mu baki daya”.
Mafi yawan Hausawa da ke zaune a Apata masu kasuwancin kayan abinci ne da ake kawowa daga Arewa. Wakilinmu ya zanta da wasu daga cikinsu da suka nuna goyon bayansu ga Sarki Sahabi, wanda suka bayyana da mutum mai kwatanta gaskiya da adalci, mai dogara da sana’arsa ta leburanci ba tare da ya nemi abun hannun jama’a ba. Haka nan sun yaba da kokarinsa na ganin bunkasar harkokin kasuwancin mutanensa da kyautata zamantakewa da jama’ar gari.