Rikicin shugabanci ya sake kunno kai a kasuwar Ladipo

Har yanzu tsugune ba ta kare ba dangane da rikicin shugabancin kasuwar kayan motoci ta Ladipo da ke Jihar Legas inda wasu ’yan kasuwar suka yi barazanar sanya kafar wando daya da sababbin shugabanin da aka nada kwanan nan.Wasu daga cikin ’yan kasuwar da ke goyon bayan shugabancin tsohon shugaban kasuwar mai suna Jonathan Okoli […]

Rikicin shugabanci ya sake kunno kai a kasuwar Ladipo
Rikicin shugabanci ya sake kunno kai a kasuwar Ladipo

Har yanzu tsugune ba ta kare ba dangane da rikicin shugabancin kasuwar kayan motoci ta Ladipo da ke Jihar Legas inda wasu ’yan kasuwar suka yi barazanar sanya kafar wando daya da sababbin shugabanin da aka nada kwanan nan.
Wasu daga cikin ’yan kasuwar da ke goyon bayan shugabancin tsohon shugaban kasuwar mai suna Jonathan Okoli sun yi kememe cewar ba sa goyon bayan sabon shugabancin kasuwar da gwamnati ta nada.
To sai dai gwamnatin jihar ta mayar da martanin cewa tana daukar matakan da za su kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasuwar.
Sakataren kungiyar Aguiyi Ironsi ta kasuwar mai suna Cif Christian Ibegbunam da sakataren kudi, Mista bincent Nwosu da ke goyon bayan tsohon shugaban kasuwar Jonathan Okoli sun bayyana cewa sabanin rahotannin da ke nuna cewa an sami zaman lafiya a kasuwar yanzu ’yan kasuwar na yin harkokinsu cikin fargaba ne.
Cif Ibegbunam ya ce, “Babu zaman lafiya, babu kwanciyar hankali a kasuwar Ladipo. Rahotannin da wasu jaridu suka buga cewa an sami daidaito da zaman lafiya da kwanciyar hankali karya ne kuma an shirya shi ne don a yaudari hukumomi da jama’ar gari”.
Ya ci gaba da cewa, “Rahotannin sun fito ne daga banagaren da ba sa kaunar shugabanmu Jonathan Okoli kuma su ne suka nada kansu da karfi da yaji don jama’a ba sa son su. Su ne suka kai Okoli kara kotu har aka daure shi a kurkuku ba tare da wata hujja ta gaskiya ba. Idan suna son a yi zaman lafiya su je su janye karar da suka kai kotu su ce sun janye shari’ar da suke yi da Okoli, sai mu yarda da su, mu zauna lafiya da su, amma idan ba haka ba, ba za mu taba amincewa da mulkiinsu ba har abada”.
Ya zargi sababbin shugabanin da karbar kudi  daga hannun ’yan kasuwar tare da mayar da su bayinsu ba tare da wata hujja ba.
To sai dai daya daga cikin sababbin shugabanin kasuwar mai suna Animelu ya karyata zargin da aka yi, inda ya ce maganar ba ta da makama bare madafa.
“Zargin karya suke yi, duk abin da suka fada maka karya ne. Ni dai ina rokonsu su zo mu tafi tare don mu ciyar da kasuwar Ladipo gaba kowa ya sami arziki da kwanciyar hankali. Su sani ba a samun arziki cikin tashin hankali, ana samun arziki ne cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya”. Inji shi.