Rikicin Shugabancin Coci ya jawo raunata mutane da kone-kone a Saminaka
Rikicin shugabanci na kasa da ke faruwa a Cocin Assamblies Of God a tsakanin bangaren Rabaran Chidi Okoroafor da Rabaran Paul Emeka da ya watsu zuwa sassan cocin a kasar nan, ya yi sanadin raunata mabiya cocin da dama tare da kona gidaje biyu a safiyar Lahadin da ta gabata a garin Saminaka da ke […]
Rikicin shugabanci na kasa da ke faruwa a Cocin Assamblies Of God a tsakanin bangaren Rabaran Chidi Okoroafor da Rabaran Paul Emeka da ya watsu zuwa sassan cocin a kasar nan, ya yi sanadin raunata mabiya cocin da dama tare da kona gidaje biyu a safiyar Lahadin da ta gabata a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna.
Sama da shekara daya da rikicin ya ki ci, ya ki cinyewa a yankin Saminaka, tsakanin magoya bayan shugaban cocin na gundumar Saminaka Rabaran Haruna Tutu da ke bangaren Rabaran Chidi Okoroafor da Rabaran Simon Jimo da ke bangaren Rabaran Paul Emeka da shi ma yake shugabancin cocin a Saminaka, ya sa gwamnatin Jihar Kaduna rufe cocin da makarantunsa da ke Saminaka zuwa lokacin da za a sasanta.
To, amma duk da wannan mataki da gwamnatin ta dauka sai da aka samu tashin rikici, kuma wani da rikici ya faru a kan idonsa, ya shaida wa wakilinmu cewa a ranar Lahadin makon jiya ne aka ga alamun rikicin, inda wasu daga cikin mabiya cocin, suka je suka balle makullinsa. Ya ce bayan haka cikin dare a ranar Asabar da ta gabata an ga bangarorin mabiya cocin, sun zo daga wurare daban-daban n yankin sun mamaye cocin.
Ya ce a safiyar Lahadin bangarorin sun kaure da fada, tare da jefe-jefe da duwatsu da sare-saren juna da makamai, duk da hakurin da aka yi ta ba su, amma ba su bar fadan ba, sai da jami’an tsaro suka zo suka tarwatsa su da hayaki mai sa kwalla.
Mista Dabid Daniel, malami a babbar makarantar nazarin Baibul na cocin da ke Saminaka da ke bangaren Rabaran Haruna Tutu, ya ce babban abin da ya kawo rikicin shi ne ana zuga bangaren Rabaran Paul Emeka daga sama ne.
Ya ce gwamnati ta kulle cocin na Saminaka, kuma ta ce kada a bude sai an gama shari’ar da ake yi a sama, domin a samu zaman lafiya. Amma sai ’yan kwanakin nan suka zo suka ce ba su yarda ba, suka je suka balle kwadon da aka kulle wurin, suka ce dole sai sun shiga sun yi ibada. Daga nan suka fara kone-kone suka lalata gonar masarar da aka shuka a wurin, suka kona gidan Faston da ke wurin kuma suka je gaba suka kona gidan wani Faston coci, kuma suka ji wa mutanenmu raunuka kafin jami’an tsaro su zo su tarwatsa su.
Ya yi kira ga ’yan bangarensu su yi hakuri da abin da ya faru, kuma ya bukaci gwamnati ta duba ta ga abin da za ta iya yi da mutanen da suke son su kawo tashin hankali.
Wani mutum da ya nemi a sakaya sunansa dake bangaren Rabaran Simon Jimo ya yi zargin cewa bangaren Rabaran Tutu ne suka tayar da rikicin. Ya ce bangaren Rabaran Tutu ya yi noma a harabar cocin bayan gwamnati ta rufe cocin, kuma ya ki ya ajiye motocin cocin da suke hannunsa.
Ya yi kira ga gwamnati ta yanke hukunci kan lamarin a bai wa mai gaskiya gaskiyarsa, kuma a hukunta wanda ba ya da gaskiya don kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Mai martaba Sarkin Saminaka, Alhaji Musa Muhammad Sani ya nuna matukar bakin cikinsa kan faruwar lamarin inda ya shaida wa wakilinmu cewa bai kamata a kawo wa garin wannan matsala ta shugabanci da ke faruwa a wani wuri ba, musamman ganin suna zaune lafiya a yankin.
Ya ce ganin rikicin ya yi kamari ne ya sa gwamnatin jihar ta rufe cocin gudun tashin hankali kuma kowane bangare ya yarda da rufewar.
Ya bukaci gwamnati ta dauki matakin da ya kamata kan rikicin domin a samu zaman lafiya a tsakanin mabiya cocin.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna DSP Zubairu Abubakar kan lamarin ta waya, amma hakan bai samu ba. Amma wata majiya ta ’yan sanda ta tabbatar wa wakilinmu cewa jami’an tsaro sun kama wadansu daga cikin wadanda ake zargi da tayar da rikicin domin ci gaba da bincike.
Al’amura sun daidaita bayan girke jami’an tsaro a harabar cocin da sassan garin.