Rikicin siyasa tsakanin Kwankwaso, Shekarau da Ganduje na hana Kano ci gaba – Garo
Garo, ya koka kan yadda wasu jihohi ke samun tagomashi saboda haɗin kan tsofaffn gwamnoninsu.
Tsohon Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna na Jam’iyyar APC a 2023, Murtala Sule Garo, ya yi kira ga tsofaffin gwamnonin Jihar Kano, da su manta da banbance-banbancen siyasa su haɗa kai domin ci gaban jihar.
Wannan na cikin wani bidiyo wanda ɗan siyasar ya yi kira ga tsofaffn gwamnoni da su haɗa kai don ciyar da jihar gaba.
- Hotunan zanga-zangar tsofaffin sojoji Abuja
- Boko Haram ta mamaye sansanin sojoji ta sace makamai a Borno
Garo ya nuna damuwa kan rashin jituwa tsakanin Rabiu Kwankwaso, Malam Ibrahim Shekarau, da Abdullahi Ganduje, wanda a cewarsa hakan na haifar da cikas ga ci gaban Kano.
Ya ce, “Abin takaici ne ganin jihohi kamar Zamfara, wacce ba ta kai Kano ci gaba ba, amma suna samun ci gaba saboda tsofaffin gwamnoninsu suna haɗa kai suna bayarda gudunmawa.
“Amma a nan Kano, tsofaffin gwamnonin ba sa haɗuwa don tattauna matsalolin da suka shafi jihar.”
Garo ya yi kira ga tsofaffin gwamnonin da su fifita muradun Kano a kan bambance-bambancensu.
Ya ce: “Idan da gaske suna son Jihar Kano, ya kamata su haɗa kai su yi aiki tare domin ci gabanta.
“Haɗin kai tsakanin shugabanni shi ne ginshiƙin samun nasara.”
Har ila yau, ya yaba wa ‘yan majalisar dokokin Jihar Kano kan haɗin kan da ke tsakaninsu, inda ya yi kira ga sauran ’yan siyasa su koyi da su.
Garo ya gargaɗi masu ƙoƙarin kawo rashin jituwa tsakanin mambobin majalisar.
Ya kuma bayyana cewa idan aka ci gaba da irin wannan haɗin kai, babu shakka Kano za ta samu ci gaban da ba a taɓa gani ba.