Rikicin siyasa ya ci rayuka 1,525 a Najeriya —Rahoto
Daga hawan Buhari zuwa yanzu, ’yan ta’adda sun kashe mutum 55,430 a sassan Najeriya.
Akalla mutum 1,525 aka kashe a Najeriya a sakamakon rikice-rikicen siyasa a manyan zabuka biyar da aka gudanar a kasar.
Rahoton da Cibiyar Tony Blair ta fitar ya bayyana cewa alkaluman kashe-kashe da aka samu a shekaru 25 da suka gabata abin damuwa ne lura da karatowar babban zaben 2023 a kasar.
- NAJERIYA A YAU: Matsayin Kuri’ar ’Yan Gudun Hijira A Zaben 2023
- Senegal: Kasar Afirka ta farko da ta ketare zuwa zagayen ’yan 16 a Gasar Kofin Duniya
Rahoton na zuwa ne mako biyu bayan Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ya ce a cikin kwana 50 an samu tashe-tashen hankula 52, yana mai gargadi cewa idan ba a dauki mataki ba, hakan zai iya kawo tasgaro ga zaben 2023.
Cibiyar ta bayyana fargaba game da yiwuwar rikice-rikice su haddasa matsaloli a lokacin zaben, ganin yadda ayyukan Boko Hara da kungiyar IPOB da kuma ’yan bindiga suka hana kasar sakat.
Ta kara da cewa kungiyoyin fararen hulda da jam’iyyun siysa da jami’an tsaro na nuna damuwarsu kan yadda rikice-rikicen zabe da sauran matsaloloin tsaro ke addabar kasar.
Matsalolin tsaro
Matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya sun hada da ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya da kuma ta’addancin kungiyar a-ware ta IPOB a yankin Kudu maso Gabas.
Wani rahoto da kafar Daily Trust ta samu ya nuna cewa a rikicin zaben 2011 ne aka fi samun asarar rayuka a Najeriya, inda aka kashe mutum 800.
Na biye da shi shi ne zaben 2003, inda mutum 300 suka rasa rayukansu, na uku shi ne zaben 2019 da aka kashe mutum 145, sannan aka yi asarar rayuka 100 a zaben 2015.
A 2003 an rasa mutum 100 bayan a zaben 1999 mutum 80 sun rasa rayukansu sakamakon rikice-rikice siyasa.
Rahoton ya nuna daga hawan gwamnatin Buhari a 2015 zuwa yanzu, ’yan ta’adda da sauran masu aikata manyan laifuka a sun kashe mutum 55,430 a sassa daban-daban na Najeriya.
Kashe-kashe mafiya muni
Bincike ya gano rikicin siyasa mafi muni shi ne wanda ya biyo bayan zaben 2011, wanda shugaban kasa mai ci a lokacin, Goodluck Jonathan ya lashe.
Sanarwar faduwar dan takarar babbar jam’iyyar adawa, Muhammadu Buhari, ta haifar ta tarzoma ta tsawon kwana uku, tare da yin ajajlin mutum 800, wasu 65,000 kuma suka rasa muhallansu.
Duk da cewa a hukumance babu alkaluman tarzoma da rikice-rikicen kabilanci daga 2015 zuwa 2019 a Najeriya, amma Kungiyar Sanya Ido kan Zabuka ta Tarayyar Turai (EU), ta ce, “rikici da barazanar magoya bayan jam’iyyu ga masu zabe da jami’an hukumar zabe ta INEC” sun dabaibaye zaben 2019.
Rahoton na EU ya ce an kashe akalla mutum 145 a rikice-rikice masu alaka da zaben 2019, adadin da ya haura na 2015 da mutum 100.
Amma kasancewar manyan ’yan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na PDP, dukkansu Musulmi ne, kuma ’yan kabilar Fulani, ya takaita tashin hankali bayan zaben.
Hakazalika, amincewa da shan kaye a hannun Muhammadu Buhari na APC da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi, a zaben 2015, ya taimaka wajen kawar da tashin irin rikicin da aka gani a 2011.
Zaben 2023
Sai dai a yayin da zaben 2023 ke kara karatowa, duk da cewa manyan ’yan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki da Atiku na babbar jam’iyyar adawa ta PDP Musulmi ne, amma kabilarsu ba daya ba, haka ma yankin da suka fito daban-daban.
Haka kuma, sauran manyan ’yan takarar kujerar biyu, Peter Obi na Jam’iyyar LP Kirista ne daga yankin Kudu maso Gabas, shi kuma Sanata Rabi’u Kwankwaso na NNPP kuma Musulmi ne daga Arewa ta Yamma kuma kowannensu na da dimbin mabiya da ake ganin sun tsaya kai da fata.
Masu sharhi na ganin akwai bukatar yin gagarumin aiki na tabbatar da aminci da ganin cewa ’yan siyasa sun karbi sakamakon zaben 2023, idan ba haka ba, akwai yiwuwar abin da ya faru bayan zaben 2011 ya maimaita kansa.