Rikicin siyasa ya jefa Benezuela cikin rudu da rashin tabbas

A watan Janairun nan ne aka rantsar da Shugaban Kasar Benezuela, Mista Nicolas Maduro domin ya ci gaba da mulki a karo na biyu. Zabensa dai ya haifar da rudani da cece-ku-ce inda babbar jam’iyyar adawar kasar ta kaurace wa zaben. Bayan an kammala zaben, wanda Shugaba Maduro ya lashe, sai aka wayi gari da hayaniya […]

Rikicin siyasa ya jefa Benezuela cikin rudu da rashin tabbas

Rikicin siyasa ya jefa Benezuela cikin rudu da rashin tabbas

A watan Janairun nan ne aka rantsar da Shugaban Kasar Benezuela, Mista Nicolas Maduro domin ya ci gaba da mulki a karo na biyu.

Zabensa dai ya haifar da rudani da cece-ku-ce inda babbar jam’iyyar adawar kasar ta kaurace wa zaben.

Bayan an kammala zaben, wanda Shugaba Maduro ya lashe, sai aka wayi gari da hayaniya da zanga-zangar rashin amincewa da sakamakon zaben.

Daga bisani shugaban ’yan hammayar kasar, Juan Guaido ya ayyana kansa a matsayin shugaban riko na kasar.

Bayan ya sanar da kansa a matsayin sabon Shugaban Kasa, sai kuma Kotun Kolin Kasar ta sanar da hana jagoran ’yan hamayyar barin kasar sannan ta kwace kadarorinsa.

Tuni Amurka da wasu kasashe suka nuna goyon bayansu ga shugaban ’yan hamayyar Juan Guaido tare da amincewa da shi a matsayin Shugaban Kasar. Sai dai Rasha da wasu kasashe suna goyon bayan Shugaba Nicolas Maduro.

Sannan Mai ba Shugaban Amurka Shawara kan Harkokin Tsaro, Mista John Bolton ya gargadi Babban Jojin Kasar Benezuela cewa matukar aka ci gaba da muzguna wa Juan Guado ta hanyar hana shi fita daga kasar, to lallai akwai mummunan sakamakon da zai iya biyowa baya.

Wannan mummunan sakamakon dai kamar yadda wasu rahotanni suka nuna, zai kunshi sanya wa kasar takunkumin karya tattalin arziki da sauransu.

A wata hira da ya yi da kafafen watsa labarai, Mista Maduro ya ce a shirye yake ya tattauna da ’yan hamayya.

“A shirye nake in zauna a teburin sulhu da ’yan hamayya domin tattaunawa kan makomar Benezuela,” inji shi, a wata hirar da ya yi da kamfanin Dillanacin Labaran Rasha (RIA) a Caracas kamar yadda BBC ya ruwaito.

’Yan hamayyar dai sun gudanar da zanga-zangar lumana ta awa biyu a shekaraniya Laraba.

Wasu kasashen Arewaci da Kudancin Amurka sun yi watsi da duk wani yunkurin tsoma bakin sojojin waje cikin rikicin kasar ta Benezuela.

Jami’an gwamnatin Amurka sun ce za su yi amfani da duk wata dama wajen kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Rikicin na Benezuela ya yi kamari har ta kai ba ma Amurka ba, wasu kasashen Turai ma sun amince da jagoran ’yan adawar kasar a matsayin Shugaban Kasar na ainihi ba Nicolas Maduro ba.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani taron gaggawa kan batun.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya sanar da Majalisar Dinkin Duniya cewa lokaci ya yi da ya kamata a goyi bayan wani bangare a rikicin siyasar Benezuela. Sakataren ya ambaci Shugaba Kasar Nicolas Maduro a matsayin wanda lokacinsa ya wuce.

Ya ce tsohuwar gwamnatin Maduro ta dade tana cin zarafin al’ummar kasarta, “A kokarin da suke yi na samun abinci da rayuwa.”

Birtaniya da Faransa da Jamus da kuma Spain na cikin kasashen da suka bi sahun Amurka wajen amincewa da jagoran ’yan adawan kasar Guaido a matsayin Shugaban Kasar na riko, amma kuma idan Maduro bai nemi a shirya sabon zabe ba a cikin kwana takwas.

Har yanzu Maduro na da sauran masu mara masa baya – musamman ma Rasha. Jakadanta a Majalisar Dinkin Duniya Bassily Nebenzia ya soki gwamnatin Shugaba Trump, inda ya ce ta shirya juyin mulki ne kawai a Benezuela.

Shi ma Shugaba Maduro ya zargi Amurka da kokarin juyin mulki a kasar, inda da kansa ya ce Dala miliyan 20 da Amurka ta yi alkawarin samarwa domin ayyukan taimakon jinkai ga sabuwar gwamnatin rikon kwarya “Sun yi kadan a matsayin lada ga masu son juyin mulkin.” Kuma Ministan Harkokin Wajen Benezuela ya yi watsi da bukatar kasashen Turai na a shirya wani sabon zabe a kasar nan da kwana takwas.

A wata sanarwa kuma, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bukaci ’yan kasarta da su guji zuwa Benezuela saboda karuwar aikata miyagun laifuffuka .

Sanarwar ta ce, har taimako daga ofishin jakadancin Amurka an hana a bai wa Amurkawa, kuma idan har ziyarar ta zama dole to lallai su sanar da ofishin jakadancin kan ina za su je, sannan su guji fita da daddare kamar yadda kafar labarai ta TRT ta ruwaito.