Rikicin Sudan ta Kudu darasi ne ga Najeriya – Balarabe Musa

Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa yana daya daga cikin ’yan siyasa masu ra’ayin ci gaba, tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna kwararren akanta ne da ya samu horo a Landan. A tattaunawa ta musamman da Aminiya ya tabo cikar Najeriya shekara 100 da harkokin siyasar kasar nan, inda ya ce abin da ke faruwa a Sudan a […]

Rikicin Sudan ta Kudu darasi ne ga Najeriya – Balarabe Musa

Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa yana daya daga cikin ’yan siyasa masu ra’ayin ci gaba, tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna kwararren akanta ne da ya samu horo a Landan. A tattaunawa ta musamman da Aminiya ya tabo cikar Najeriya shekara 100 da harkokin siyasar kasar nan, inda ya ce abin da ke faruwa a Sudan a Kudu darasi ne ga masu kiran a wargaza Najeriya:

Aminiya: A ranar 1 ga Janairun nan ne Najeriya ta cika shekara 100, inda za a gudanar da bikin hakan a watan gobe, me za ka ce kan alfanu da rashin alfanun dunkule ta a matsayin kasa daya?
Balarabe Musa: Idan ana batun hade Najeriya a 1914, za mu iya cewa hadewa ko dunkule Najeriya a matsayin kasa daya abu ne da za a yi murna domin ya haifar da alheri ga jama’a, koda dai ba wannan ne niyyar gwamnatin mulkin mallaka ta Birtaniya wadda ta hade Kudu da Arewa ta kira Najeriya ba. Turawan mulkin mallaka suna da nasu burin, amma hakan ya zama alheri ga jama’ar kasar domin a dinke su wuri daya. Kuma muna godiya ga Allah kan wannan baiwa da Ya yi ga jama’ar kasar. Kuma ko su gwamnatin Birtaniya muna yi mata godiya kan yin hakan duk da cewa suna da dalilinsu da ba mamaki ya bambanta da abin da ke faruwa. Kuma muna godiya ga wadanda suka jagoranci kwato wa kasar nan ’yanci wadanda suka ci gaba tare da karfafa kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya a lokacin mulkin ’yan mallakar da kuma Jamhuriyya ta Farko.
Aminiya: Amma akwai masu kiraye-kirayen a wargaza Najeriya?
Balarabe Musa: Akwai mutanen da suke ganin an tilasta hade Najeriya ce, wannan gaskiya ce, amma kowace kasa a duniya tana samuwa ta hanyar amfani da karfi ta wannan hanya ko wata hanyar. kasashen da suka ci gaba kamar manyansu, kamar Birtaniya da Faransa da Amurka da China da Rasha da sauransu ba wanda yake batu kan hadewa yankunansu su zama kasa. Amma kasashe irin Najeriya da suka gaza cimma nasarar da ta kamata ke babatu kan hade kasar wuri daya. Kodayake za a iya cewa ko a kasashen da suka ci gaba kamar Birtaniya har yanzu ana kiraye-kirayen a duba tilasta hade yankunan da suka zama kasar, misali yankin Scotland yana yakin neman ’yanci, amma idan suka ga kalli gwagwarmayar mutanen Scotland za su ga saboda abubuwan da muka yi watsi da su ne a nan.
Ba suna magana ne kan a wargaza gwamnatin Birtaniya ko a raba su kacokan da kasar ba, akwai wasu abubuwa da za su ci gaba da kasancewa koda Scotland ta samu ’yancin kanta. Ke nan ta wani gefe koda kasashen da suka ci gaba za ka ga ana samun kiraye-kirayen a kekketa kasar ko a wargaza ta, wannan hali ne na dan Adam. Amma za ka iya ganin hadewar ta sha bamban da ke akwai a Najeriya. A kasashen da suka ci gaba, koda za su wargaje ko su wasu kasashe su samu ’yanci, kasashen za su iya dorewa saboda sun kai wani mataki na ci gaba kamar kasashen Czechoslabakia da tsohuwar Tarayyar Sobiyet kai koda Poland ma ta kai wani matsayi na hadewar da ta ci gaba. Amma game da Najeriya, babu wani abu mabambantan sassan za su iya yi, maimakon haka  za su koma baya ne kamar yadda lamarin yake a Sudan ta Kudu ’yar karamar kasa. Amma wargajewar Najeriya babban lamari ne. Wargajewar Najeriyya ba zai yiwu ba, sai ta hanya ko bayan an gwabza dogon yakin basasa an wahala. Saboda muna raina matakin tattalin arziki da rayuwa da siyasar Najeriya, matsalarmu ita ce irin shugabannin da tsarinmu ke haifar mana na mayar da mu baya. Abin tambaya shi ne ko za mu iya magance matsalolin rayuwa da tattalin arziki da tsarin zabe wanda ke tafiyar duk harkokin ci gaban kasar. Domin na farko, an gina su ne kan son zuciya, na biyu jama’a ko sukan zo ne afke su ne kai-tsaye suke yi mana illa a halin yanzu da suke haifar mana da yunwa da rashin zaman lafiya da almundahana da sata da barnata dukiyar kasa da sauransu. Kuma idan za iya magance wannan hali, mu gyara shugabanci tare da kawo ci gaban da ya kamata, kamar yadda kasashen da suka ci gaba suka samu babu bukatar a sake duba zaman Najeriya a matsayin kasa daya.
Aminiya: Kana da ra’ayin cewa ’yan Najeriya su dubi gaba ke nan tare yin gyara?
Balarabe Musa: Eh, ina son kada a bar wasu daidaiku su yi wasa da makomar Najeriya, ba su wuce rabin kashi daya ba, kuma suna bin son rayukanku ne da burace-burace ko wasu ’yan abubuwan da za su samu ke sanya su haka.
Aminiya: Idan wargajewar ta faru, yaya kake ganin Arewa za ta kasance?
Balarabe Musa: Yaya kowane bangare zai kasance idan muka samu kasashe 10? Hakika kowace kasa za ta koma baya, ba wadda za ta samu wani ci gaba a nan kusa. Saboda mutanen da suke hade kasa daya sun yi nisa sosai saboda ba mu kai matsayi na ci gaba da kasashen za su mike kamar yadda jamhuriyoyin tsohuwar Tarayyar Sobiyet suke mikewa, saboda an aza harsashin da kasashen za su kafu a kai.  Kuma ko su ma akwai matsaloli, Ukraine ce kawai ta fi samun nasara a bayan Rasha a fannin kishin kasa amma duk da haka tana ta’allake da Rasha a wasu abubuwa. Idan haka ta faru a Najeriya, koda shiyyoyin nan shida na Najeriya ba yadda daya za ta ci gaba ba tare da dayar ba. Kowacce za ta fuskanci wahala. Kowa ya san Kudu ta dogara ne da Arewa a bangaren abinci, Kudu za ta dauki dogon lokaci da zuba dimbin dukiya kafin ta iya samar da wadataccen abincin da take bukata. Mu kuma a Arewa manyan ’yan kasuwa da masu dukiya da manyyan shugabannin Arewa sun dogara ne kan shigo da kaya daga waje domin irin rayuwar da suke yi.  A yanzu kudin da ake shigo da kayan nan ba daga noma da Arewa ta dogara das hi ake samunsu ba, suna zuwa ne daga man fetur da ake samu a Kudu.   
Don haka misali idan Najeriya ta rabe biyu tsakanin Kudu da Arewa, Arewa za ta sha wahalar shigo da irin wadannan kaya da ’yan bokon Arewa ke bukata domin jin dadin rayuwarsu. Ka ji mamakin yadda wahalar da ’yan bokon Arewa za su shiga idan ba a shigo da abinci da kayan alatu daga waje kamar motoci da kayan gini, haka lamarin zai kasance saboda kudin musaya da ake samu albarkacin man fetur ba zai zo Arewa ba, tilas Arewa ta nemo madadi ta komawa ga noma da ta watsar. Babu wadatattun masana’antu a Arewa. Masana’antun Najeriya ba su iya gasa koda a cikin Najeriyar balle Afirka ta Yamma. Don haka tattalin arzikinmu ya dunkule tare da sajewa a tsakanin sassan kasar a shekara 100 da suka gabata, zai zamo kamar kashe kai ne ga kowane bangaren Najeriya ya nemi ballewa.
Aminiya: Ya dace a yi bikin haka kamar yadda gwamnati ta shirya?
Balarabe Musa: Eh, ya cancanta a yi biki, sai dai kada a kashe kudin da ya wuce kima, kamar na shekara 50 da samun ’yancin kai wanda bai da wani alfanu. Na farko muna godiya ga Allah Wanda cikin rahamarSa Ya wadata mu da babbar kasa mai dukiya, sannan muna godiya ga mutanen Birtaniya da suka samu hikimar yin haka domin biyan bukatar kansu. Domin mun samu haka ne ba tare da yaki ba, kamar yadda ke akwai a wasu yankuna. Kuma muna godiya ga wadanda suka kwato mana ’yanci ka sadaukarwar da suka yi a lokacin mulkin mallaka da Jamhuriyya ta Farko wadda ta rike Najeriya har zuwa yau, domin da ba su yi haka ba, wannan Najeriyar za ta wargaje tun lokacin, domin man fetur da ya rike kasar nan ba a gano shi ba, sai wajejen 1970.
Aminiya: Kana goyon bayan taron kasa?
Balarabe Musa: Ina ganin babban taron kasa mai ’yanci yana da muhimmanci, amma a yanzu ba zai yiwu ba, saboda hanya c eta juyin juya-hali, domin yana nufin a jingine shugabannin da suke kan gado bangaren zartarwa da na majalisa da na shari’a domin amfanin majalisar juyin juya-hali. Ba za ka samu haka a yanzu ba, sai an yi juyin juya-hali, ba za ka zauna a kan teburi ka gudanar da babban taron kasa ba. Wajibi ne sai an samu juyin juya-halin rayuwa. A yanzu ba na ganin tilas a yi shi, za a iya kyale shi mu samu wani taron kasa. Kuma taron kasar da muka samu a yanzu ba zai kasance bisa yadda Shugaban kasa ke sha’awa ba. Muna bukatar taron kasa ne da mutanen Najeriya masu ’yanci za su gudanar da shi, duk masu rajistar jefa kuri’a a Najeriya da suke aiki domin jama’a kamar kungiyoyin kare hakkin jama’a da kungiyar ’yantattun jama’a (SPC) da shugaban Majalisar Dattawa da Shugaban Majalisar Wakilai da Babban Jojin Najeriya su gudanar tare da jagorancin taron. Yana nufin mu daina tsari na dora wa juna laifi kan rashin ci gaban kasar nan. Mu amince kasar nan ta gaza, bangaren majalisa da na shari’a sun gaza, mutane masu ’yanci suna da ikon da za yanke shawara kan makomar Najeriya. Kuma domin a kauce wa zargi bari a kawo bangarorin biyar su zauna tare su yanke shawara kan taron kasar su gudanar da shi tare da jagorantarsa. kungiyoyi biyar na mutane masu ’yanci ta hannun kungiyar Lauyoyi ta kasa da kungiyar kwadago ta kasa da kungiyar Manyan Ma’aikata da kungiyar ’Yan Jarida ta kasa da Shugaban Majalisar Dattawa da na Wakilai da Babban Joji su kafa wani kwamiti da zai yanke shawara kan ko mu gudanar da taron kasa kuma a kafa bangarorin da za su shirya taron kasar ya yanke shawara kan wakilai da yadda za a zabe su. Wakilai biyu daga kowace karamar hukuma daga kananan hukumomi 774 kimanin 1500 da wasu wakilan jihohi da sauran masu sha’awa ciki har da jam’iyyun siyasa da kungiyoyin masu masana’antu da na ’yan kasuwa da Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci da kungiyar Kiristoci ta Najeriya, hatta kungiyoyin kabilu sun tura wakilai na musamman dari biyar. Najeriya za ta iya gudanar da taron kasa mai mutum dubu biyu, domin ko jam’iyyun siyasa kan iya gudanar da taron mutum dubu biyu a manyan tarurrukansu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno