Rikicin Sudan ya sa farashin raguna tashin gwauron zabo a Saudiyya
Masana tattalin arziki sun ce rikicin siyasar da ke aukuwa a kasar Sudan na iya jawo tashin farashin dabbobin layya da kimanin kashi 80 cikin 100 a kasuwannin kasar Saudiyya.Saudiyya tana shigo da kimanin kashi 40 cikin 100 na dabbobi ne daga kasar Sudan, kuma a yayin da za a samu karuwar bukatar dabbobi domin […]
Masana tattalin arziki sun ce rikicin siyasar da ke aukuwa a kasar Sudan na iya jawo tashin farashin dabbobin layya da kimanin kashi 80 cikin 100 a kasuwannin kasar Saudiyya.
Saudiyya tana shigo da kimanin kashi 40 cikin 100 na dabbobi ne daga kasar Sudan, kuma a yayin da za a samu karuwar bukatar dabbobi domin Sallar Layya, kasuwar dabbobi za ta hadu da matsala saboda fataken dabbobi ba za su iya sayo su daga kasar Siriya da ita ma ke fama da rikici ba.
Tuni dai kasar Saudiyya ta sayo dabbobi miliyan biyu daga kasashen Sudan da Somaliya domin amfani da su a lokacin aikin Hajjin bana.
Wani masani tattalin arziki mai suna Fadal Abu Ainain ya shaida wa kafar labarai ta Arab News cewa “Farashin dabbobi ya riga ya tashi da kashi 30 cikin 100 bayan fataken dabbobi ’yan kasar sun daina shiga da dabbobin daga kasar Siriya da yaki ya daidaita. Sannan rikicin siyasa da ya auka wa Sudan zai yi matukar jawo cikas ga shiga da dabbobin zuwa Mulukiyyar Saudiyya.”
Ya kara da cewa, “Wajibi ne Mulukiyyar ta fara nema sababbin kasuwannin sayo dabbobi domin kauce wa karancinsu, wanda zai tsawwala farashinsu da haifar da tsadar nama.”
Shugaban Kwamitin samar da dabbobi na kungiyar ’Yan da Masu Masana’antu na Jiddah (JCCI), Sulaiman Al-Jabri, ya shaida wa kafar labaran cewa, “Saudiyya ta shigo da dabbobi miliyan biyu domin aikin Hajjin bana. Kuma muna sa ran farashin raguna ba zai tsallake Riyal 900 ba, (kimanin Naira dubu 36) gwargwadon irin ragon da za a saya.”
Ya ce, “Rikicin siyasar Sudan ba zai jawo tashin farashin dabbobi a cikin gida ba. Saboda gwamnatin Saudiyya ta tsara hanyoyin shigo da dabbobi daga sababbin kasuwanni. Kasuwannin cikin gida suna shigo da kimanin kashi 75 cikin 100 na dabbobin ne daga kasashen waje.”
Sudan tana sa ran samun kusan Dala miliyan 408 (kimanin Naira biliyan 65 da miliyan 280) daga fitar da dabbobi zuwa kasashen zuwa karshen watan Nuwamba, inda ta samu karin kashi 20 cikin 100 kan abin da ta samu a bara.
kasar Sudan dai tana fuskantar matsalar tattalin arziki tun daga lokacin da kasar Sudan ta Kudu wadda take da kashi uku bisa hudu na man tsohuwar kasar ta samu ’yanci a bara karkashin yarjejeniyar kawo karshen yakin basasa na shekaru da aka cimma a shekarar 2005.