Rikicin Syria: An watsa guba a Aleppo
Mutum 80 sun jikkata bayan da aka yi zargin cewa dakarun gwamnatin Syria sun watsa bama-bamai masu ’ya’ya da suke dauke da gubar sinadarin Chlorine daga cikin jirgin helikwafta a garin Aleppo.Gidan rediyon BBC Landan, ya ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa, masu aikin jinkai na gaggawa sun ce mutane sun rika fuskantar matsala da numfashi […]
Mutum 80 sun jikkata bayan da aka yi zargin cewa dakarun gwamnatin Syria sun watsa bama-bamai masu ’ya’ya da suke dauke da gubar sinadarin Chlorine daga cikin jirgin helikwafta a garin Aleppo.
Gidan rediyon BBC Landan, ya ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa, masu aikin jinkai na gaggawa sun ce mutane sun rika fuskantar matsala da numfashi sakamakon harin da aka kai a yankin Sukkari.
Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da tabbatar da sahihancin rahoton.
Wani bincike da Majalisar dinkin Duniya ta gudanar, ya ce gwamnatin Syria ta yi amfani da sinadarin Chlorine a lokuta biyu.
Sai dai gwamnatin Syria ta sha musanta zargin da ke cewa tana amfani da makamai masu guba a yakin da take da mayakan kungiyar ISIS da na masu ra’ayin dimokuradiyya.