Rikicin Ukraine: Romaniya za ta bai wa ’yan Najeriya gurabun karatu
An fara shirye-shiryen bai wa daliban damar ci gaba da karatunsu.
Gwamnatin Tarayya ta ce ta fara shirye-shirye da kasar Romaniya domin daukar daliban Najeriya da suka tsere wa rikicin kasar Ukraine, wadanda ke son ci gaba da karatunsu a jami’o’in kasar.
Wannan na dauke ne a cikin wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Bucharest ya fitarcewa an bai wa daliban wa’adin wata guda domin yanke shawara.
- DAGA LARABA: Hanyoyin Da Labaran Karya Ke Wa Jama’a Illa
- Akwai yiwuwar mace ta zama Gwamnan Kaduna —El-Rufai
Sanarwar ta ce, “Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Bucharest a Romaniya, na farin cikin sanar da daliban Najeriya da ke ficewa daga Ukraine cewa an kammala shirye-shirye da wasu jami’o’i don ba su dakunan kwanan dalibai na tsawon wata guda.
“Duk wanda ya ke son cin wannan moriya ya tura sakon tes ga wadannan lambobi: +40 749 335 927, +40 786 091 964.”
Rikicin Ukraine ya sanya daliban Najeriya da dama da ke karatu a can hakura tare da dawowa gida Najeriya, don tsira da rayukansu.
Mako biyu ke nan da ake gwabza yaki tsakanin Ukraine da Rasha.