Rikicin Ukraine: Shugabanni Afirka Munafikai ne —Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya zargi shugabannin kasasashen Afirka da munafirci kan rikicin Rasha da Ukraine. Macron ya yi wannan suka ne a Yaounde kasar Kamaru a yayin da yake jawabi ga ’yan jarida a wata ziyarar da ya kai kasar. Shugaban na Faransa ya yi magana da kakkausar murya kan matsayar nahiyar kan […]
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya zargi shugabannin kasasashen Afirka da munafirci kan rikicin Rasha da Ukraine.
Macron ya yi wannan suka ne a Yaounde kasar Kamaru a yayin da yake jawabi ga ’yan jarida a wata ziyarar da ya kai kasar.
Shugaban na Faransa ya yi magana da kakkausar murya kan matsayar nahiyar kan rikicin yana mai cewa munafirci ne zalla.
Wasu kasashen na Afirka sun kame harshensu daga fitowa karara su soki Rasha kan mamayar da ta yi wa Ukaraine.
A watan Maris kasashen Afirka 17 ne suka kaurace wa jefa kuri’a a kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ke yin Allah wadai da mamayar, yayin da wasu kalilan suka amince.
Shugaban na Faransa yana ziyarar aiki ne a nahiyar a inda yake ziyarar wasu kasashe uku da faransa ta raina.