Rikicin Ukraine ya raba mutum miliyan 6.5 da muhallansu – MDD

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa yawan mutanen da rikicin Ukraine ya raba da muhallansu ya haura miliyan 6.5, kari a kan miliyan 3.2 din da suka gudu daga kasar.  Alkaluman dai na nuni da cewa kasar ta tasamma kamo Siriya a yawan mutanen da yaki ya daidaita, […]

Rikicin Ukraine ya raba mutum miliyan 6.5 da muhallansu – MDD

Yadda ‘yan Ukraine ke tururuwar ficewa daga kasar

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa yawan mutanen da rikicin Ukraine ya raba da muhallansu ya haura miliyan 6.5, kari a kan miliyan 3.2 din da suka gudu daga kasar. 

Alkaluman dai na nuni da cewa kasar ta tasamma kamo Siriya a yawan mutanen da yaki ya daidaita, wacce take da sama da mutum miliyan 13 da suka bar gidajensu zuwa wasu wuraren a ciki da wajen kasar.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata takarda da Ofishin Ayyukan Jinkai na hukumar ya fitar a ranar Juma’a.

Hukumar dai ta ambato wasu alkaluma daga hukumomin kasar, inda ta ce akalla mutum miliyan 6.48 ne suka rasa muhallan nasu ya zuwa ranar 16 ga watan Maris.

A wani labarin kuma, Shugaban Amurka, Joe Biden ya shaida wa takwaransa na China, Xi Jinping cewa kasar za ta dandana kudarta muddin ta tallafa wa Rasha a yakin da take yi da Ukraine.

A cewar wani jami’in Fadar Shugaban Amurka ta White House yayin wani jawabi ga manema labarai, ya ce Biden ya kira Mista Xi ta waya, inda ya ce tattaunar tasu cikakkiya ce.

“Za mu tsaya mu ga matakin da China za ta dauka a cikin kwanaki da watanni masu zuwa,” inji jami’in.