Rikicin Ukraine: Za a soma jigilar dawo da ’yan Najeriya gida a ranar Laraba

Muna fatan fara jigilar dawo da su gida ranar Laraba.

Rikicin Ukraine: Za a soma jigilar dawo da ’yan Najeriya gida a ranar Laraba

Zaman tattaunawa da aka yi da Kakakin Majalisar Wakilai da Ministan Harkokin Wajen Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na soma jigilar dawo da ’yan Najeriya gida da suka makale a Ukraine da ke fuskantar hare-hare daga dakarun sojin Rasha. 

Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da wakilan ma’aikatarsa suka yi da Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya, Femi Gbajabiamila a ranar Litinin.

A wani sako da Ofishin Kakakin Majalisar ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce gwamnati za ta fara aikin dawo da ’yan kasarta gida Najeriya daga ranar Laraba.

Ministan ya ce Najeriya ta kammala duk wasu shirye-shiryen dawo da ’yan kasarta gida wadanda suka makale a wasu kasashen saboda yakin Rasha da Ukraine.

“Muna fatan fara jigilar dawo da su gida ranar Laraba, muna aiki ba dare da rana don tabbatar da ranar Laraba mai zuwa mun tura jirgi ya debo su.”

Aminiya ta ruwaito cewa tun da farko dai Gwamnatin Tarayya ta sanar da aniyarta na soma dawo da ’yan Najeriya gida daga kasar Ukraine biyo bayan mamayar da Rasha ta yi wa kasar.

Gwamnati ta dauki azamar gudanar da wata jigilar jiragen sama ta musamman domin kwaso yan kasarta daga Ukraine sakamakon yadda rikici ke kara ta’azzara tsakanin kasar da Rasha.

Ministan Harkokin Wajen Kasar, Geoffery Onyeama a wata hirarsa da gidan talabijin na NTA, ya ce an tuntubi Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Kiev domin soma jigilar wadanda ke son dawowa gida Najeriya.

Ministan ya ce ma’aikatarsa na ci gaba da bibiyar duk abin da ke wakana a kasar ta Ukraine tare da shan alwashin cewa za a yi duk wata mai yiwuwa wajen bai wa ’yan kasar kariya musamman dalibai.

A ranar Alhamis ce dai Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya umarci Shugaban Masu Rinjaye na majalisar da ya gaggauta tattaunawa da Ma’aikatar Harkokin Wwajen Najeriya domin shirya yadda za a dawo da ’yan Najeriya daga kasar Ukraine da Rasha ta mamaye.

Gbajabiamila ya umarci Ado Doguwa ya tattauna da Shugaban Kamfanin Jiragen Saman Najeriya na Peace Air domin shirya yadda za a dawo da ’yan Najeriya gida.

Kasar Rasha ta mamaye wasu sassa na kasar Ukraine tun daga ranar Alhamis inda ta rika yi wa kasar luguden wuta ta sama bayan ta aika da sama da sojojinta 200,000 zuwa iyakan kasar da manyamanyan tankokin yaki

A rahotanni da ke bayyana daga kasar Ukraine an rika ganin yadda rugugin wuta na nakiyoyi da igwa igwa ta sama da kasa da sojojin kasar Rasha ke aikawa kasar Ukraine din.

Gwamnatocin kasashe da dama sun yi tofin Allah-Tsine ga wannan hare-hare na sojojin Rasha a kan kasar Ukraine.

Kasashen duniya ciki har da Amurka, Birtaniya, Faransa da sauran manya-manyan kasahen duniya na gargadin Rasha ta shiga taitayinta sannan sun bayyana cewa lallai za su saka wa kasar takunkumi masu tsauri da zai yi lagalaga da tattalin arzikin kasar.

Zuwa yanzu farashin danyen man fetur ya yi tashin gwauron zabi a dalilin wannan mamaya da Rasha ta kaiwa Ukraine.