Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Irin wannan takaddama ta taɓa tasowa a shekarun bayan a hukumomin jin daɗin alhazai na jihohin Enugu, Ribas, Anambra, Kuros Riba da Akwa Ibom.

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

An samu saɓani a Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Delta tsakanin ’yan asalin jihar da kuma baki, kan wanda ya fi cancanta ya jagoranci hukumar.

Aminiya ta samu labarin cewa, ’yan asalin jihar suna zargin cewa an fifita mutanen da ba ’yan asalin jihar ba ne wajen ba su muƙamin shugabanci.

’Yan asalin jihar sun kuma bukaci a miƙa shugabancin hukumar zuwa yankin Delta ta Tsakiya, a matsayin wani mataki na daidaita rabon muƙamai tsakanin al’ummomin jihar.

Rahotanni sun nuna cewa irin wannan takaddama ta taɓa tasowa a shekarun bayan a hukumomin jin daɗin alhazai na jihohin Enugu, Ribas, Anambra, Kuros Riba da Akwa Ibom.

Musulmi ’yan asalin jihohin sun bayyana cewa ba a samun irin wannan tsari a jihohin Arewa, inda suke cewa babu wata jiha kamar Kano, Sakkwatoo ko Zamfara da aka taɓa ba wani ɗan Kudu shugabancin hukumar jin daɗin alhazansu.

Da yake yi wa Aminiya ƙarin haske kan rikicin, jami’in hulɗa da jama’a na Majalisar Musulmin Jihar Delta, Abdulsalam Ogan, ya ce gwamnatin jihar ta shiga tsakani domin warware matsalar tare da tabbatar da adalci da zaman lafiya tsakanin al’ummar Musulmin jihar.

Ya ce saboda haka ne za a zauna da masu ruwa da tsaki a hukumar domin tattauna matsalar da kuma samo mafita mai ɗorewa.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe