Rikicin ‘yan sanda da ’yan acaba Kabu ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyu a Akwa-Ibom

Mutum biyu sun rasa rayukansu a wani dauki- ba-dadi a tsakanin ’yan sanda da ’yan acaba a Karamar Hukumar Eket,  a Jihar Akwa Ibom sakamakon rashin fahimta da ta shiga tsakanin ’yan sanda da ’yan acabar. ’Yan acabar sun zargi ’yan sanda da kashe musu abokan sana’a biyu a rikicin da suka yi da su […]

Rikicin ‘yan sanda da ’yan acaba Kabu ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyu a Akwa-Ibom

Zaki Ahmed Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Akwa Ibom

Mutum biyu sun rasa rayukansu a wani dauki- ba-dadi a tsakanin ’yan sanda da ’yan acaba a Karamar Hukumar Eket,  a Jihar Akwa Ibom sakamakon rashin fahimta da ta shiga tsakanin ’yan sanda da ’yan acabar. ’Yan acabar sun zargi ’yan sanda da kashe musu abokan sana’a biyu a rikicin da suka yi da su a ranar Talatar da ta gabata.

Bayanan da Aminiya ta samu ’yan acabar sun yi  ramuwar gayya wajen kona wata motar sintiri guda ta ’yan sanda. Abin da ya jawo rigimar ya kuma harzuka ’yan acabar shi ne ’yan sandan sun hana duk wani mai yin hayar babur yin aiki cikin dare kuma sun ce doka ta amince musu su fara haya daga karfe 6:00 na safe ne zuwa 6:00 na yamma wanda kuma ya keta dokar zai dandana kudarsa.

Wani wanda lamarin ya rutsa da shi mai suna Effiong  Okpo, ya shaida wa manema labarai cewa “A makon jiya ’yan sanda sun harbe mana abokin sana’a daya gawarsa na can a dakin ajiye gawargwaki a babban asibitin Eket. Kana kuma ranar Litinin wani dan sanda ya yi wa wani abokin sana’armu mai suna Udo Idung Udoe  dukan kawo wuka aka kwashe shi zuwa asibiti   shi ma ya mutu  lamarin da ya dada tayar mana da hankali.”

Ya ci gaba da cewa, “Mun dauki gawar zuwa ofishin ’yan sanda suka hana musu shiga ofishin suka kore mu.”

Wakilinmu ya tuntubi Mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Akwa Ibom, SP Odiko McDon game da labarin, inda ya ce  babu wani da aka kashe  zance ne kurum da kazafi irin na masu haya da babura.