Rikicin ’yan Shi’a da jami’an tsaro

Rikicin ’yan Shi’a da jami’an tsaro da ke ci gaba da wanzuwa abin jimami ne da damuwa. Lura da  cewa rikici farkonsa aka sani amma ba a san karshensa ba. Kuma in har ba a gaggauta zuba wa wutar rikicin ruwa ba, rikicin na iya daukar sabon salo ta hanyar karade kasar nan baki daya. […]

Rikicin ’yan Shi’a da jami’an tsaro
Rikicin ’yan Shi’a da jami’an tsaro

Rikicin ’yan Shi’a da jami’an tsaro da ke ci gaba da wanzuwa abin jimami ne da damuwa. Lura da  cewa rikici farkonsa aka sani amma ba a san karshensa ba. Kuma in har ba a gaggauta zuba wa wutar rikicin ruwa ba, rikicin na iya daukar sabon salo ta hanyar karade kasar nan baki daya. Domin ’yan uwan bangarorin biyu da ke sauran jihohi zai yi wuya su zura ido su ga ana kashe ’yan uwansu a Abuja su kyale. Kafin hakan ta kai ga faruwa ya kamata dattawan kasa da malaman addini da sarakuna da sauran jama’a nagari  su shiga tsakanin ’yan Shi’a da gwamnati domin a fahimci juna a samu maslaha.

Watakila hakan zai sanya jama’ar kasa sun samu saukin tashin hankalin da ke damunsu, ga tashin hankali na masu satar mutane ga na Boko Haram ga kuma na kunci da tsadar rayuwa sannan ga na ’yan Shi’a da jami’an tsaro. Shin da wane ne za su ji?

Wannan rikici gwamnati tana da laifi ’yan Shi’a suna da laifi. Haka gwamnati na da gaskiya su ma ’yan Shi’a na da gaskiya. Laifin gwamnati shi ne taki yi wa jagoran ’yan Shi’ar shari’a an garkame shi shekara da shekaru. An ki fitar da shi waje a samar masa lafiya. Ta yi watsi da umarnin wata kotu da ta ce a sake shi. Garkiyar gwamnati ba za ta sanya ido ta kyale wadansu ba su bin dokar kasa ba har su rika fada da gwamnatin duk da ita ma gwamnatin akwai inda ta taka dokar kasa. Gaskiyar ’yan Shi’ar ba za su zura ido su kyale ba su san halin da jagoransu yake ciki ba. ’Yan siyasa na yi tarurruka suna toshe hanyoyi ba tare da an tsawata musu ba. Su kuma ’yan Shi’a da sun yi nasu taron sai a ce sun toshe hanya. Laifinsu kuwa daukar doka a hannunsu. Konewa ko farfasa kayan jama’ar da ba su ji ba su gani ba sannan suna bata gine-ginen gwamnati da na sauran jama’a inda suke rubuta FREE ZAKZAKY da sauran wasu kalamai na muzanta shugabanni. A karshe ina kira ga daukacin jama’a a duk inda suke mu ci gaba da yin addu’ar Allah Ya kawo maslahar wannan lamari ya kawo wa kasarmu zaman lafiya.

 

Daga Haruna Muhammad Katsina