Rikicin ’yan Shi’a da mutanen Gyallesu ya ci mutum daya

Artabu da aka yi a tsakanin ’yan Shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky da mazauna Unguwar Gyallesu da ke yankin Tudun Wadan Zariya a Jihar Kaduna a ranar Juma’ar makon jiya ya jawo mutuwar mutum daya inda mutum 30 suka jikkata. Mazauna Unguwar Gyallesu dai na zargin ’yan Shi’a mabiya Sheikh Zakzaky na tsangwama da takura […]

Rikicin ’yan Shi’a da mutanen Gyallesu ya ci mutum daya
Rikicin ’yan Shi’a da mutanen Gyallesu ya ci mutum daya

Artabu da aka yi a tsakanin ’yan Shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky da mazauna Unguwar Gyallesu da ke yankin Tudun Wadan Zariya a Jihar Kaduna a ranar Juma’ar makon jiya ya jawo mutuwar mutum daya inda mutum 30 suka jikkata.

Mazauna Unguwar Gyallesu dai na zargin ’yan Shi’a mabiya Sheikh Zakzaky na tsangwama da takura musu ta hanyar sanya musu shingaye a hanyoyin shiga unguwar.
Wani mai magana da yawun mutanen unguwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutanen unguwar Gyallesu sun shiga tasku sakamakon yadda almajiran Malam Ibrahim Zakzaky ke takura musu ta hanyar sanya musu shingaye a hanyoyin unguwar gaba daya da mamaye musu kofofin gidajensu, ta yadda idan mutum zai shiga gidansa sai ya ce a buda masa kafin ya wuce. Ya ce haka kuma idan larura ta kama mutum don fita a cikin dare ko ya dawo cikin dare, yakan sha tambayoyi da haske-hasken fitilu, wanda hakan ya janyo tashin manyan mutane daga unguwar, kuma duk yadda aka so a fahimci juna ba a cimma nasara ba.
Ya ce akwai lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yaro ya ziyartar daya daga cikin dattawan unguwa da bai da lafiya, amma almajiran Zakzaky suka ce ba zai wuce ba, kuma hakan ya haifar da tashin hankali. “Bayan Gwamna ya gama ziyayarsa ya koma, sai samarin unguwa suka fito suka farfasa shingayen da ke unguwar, yin haka ya jawo matsalar da har yanzu ta biye da mu, ga shi an kara kwatawa a dalilin shingayen. Duk matakin da ya kamata mu dauka don a zauna lafiya ta hanyar rubuta takardu da sanar da hukumomin tsaro tunda kan DPO zuwa kan Kwamishinan ’Yan sanda da Masarautar Zazzau, har yanzu ba a samu maslaha ba, har ranar Juma’a aka yi tashin hankali mutum daya mai suna Ibrahim Isma’il na Gangare Tudun Wada da ke aikin tsaron unguwa karkashin ZAMDA ya rasu, kuma 30 suka jikkata,” inji shi.
A martaninsa ta kafafen watsa labarai, Sheikh Ibrahim Zazzaky ya ce a saninsa yana zaune lafiya da mutanen Gyallesu, inda ya ce tun shekara 20 da dawowarsa unguwar bai taba tashin hankali da wani makwabcinsa ba, kuma in akwai wata matsala sukan zauna da mutanen unguwar domin su warware abinsu. Saboda haka yana zargin jami’an tsaro ne suka kitsa haka suka turo wasu wadanda ba a san ko su wane ne ba domin su tada hankali jami’an tsaro su fake da haka su shigo su kashe shi tare da mabiyansa.
Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Zubairu Abubakar ta waya amma bai dauka ba, kuma bai mayar da sakon waya da wakilinmu ya aika masa kan lamarin ba.