Rikicin ’Yan Ta’adda: Kachalla Ɗan Ƙarami ya kashe abokin gabarsa a Zamfara

An fille kan Dangote a wani mummunan faɗa da aka gwabza a Dunmurun da ke Karamar Hukumar Zurmi a Zamfara.

Rikicin ’Yan Ta’adda: Kachalla Ɗan Ƙarami ya kashe abokin gabarsa a Zamfara

’Yan daban daji

Kasurgumin dan ta’addar da ya addabi yankin Batsari a Jihar Katsina da wani yanki na Jihar Zamfara  ya gamu da ajalinsa a hannun Kachalla Dan Karami. 

Wata majiya mai tushe daga Batsari a Jihar Katsina ta tabbatar mana da cewa Kachalla Dan Karami ya fille kan Dangote ne a wani mummunan faɗa da aka gwabza a Dunmurun da ke Karamar Hukumar Zurmi a Zamfara.

Kachalla Dankarami ya yi sanadiyar kashe Dangote ne tare da wasu kannensa guda biyu da ke addabar Jihar Katsina da wani yanki na Jihar Zamfara a safiyar ranar Lahadi da ta gabata.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Dan Karami da tawagarsa sun yi wa Dangote da yaransa kwanton ɓauna ne a daren Asabar, inda suka fara gwabzawa har safiyar ranar Lahadin da ta gabata.

Wata majiya daga jami’an tsaro ta bayyana mana cewa tun da farko dai yaran Dangote ne suka kashe yaron Kachalla Dan Karami sakamakon sace musu tumaki da aka yi.

“Abin da ya faru shi ne, ɗaya daga cikin yaran Dan Karami ya saci garken tumakin ɗaya daga cikin ’yan uwan Dangote, Sale Lamo, sai yaran Dangote suka bi sawun tumakin suka karɓo su, sannan suka kashe yaron.”

“A lokacin da abin ya faru Dan Karami yana wani gari da ake kira Rukudawa, sai aka ba shi labarin abin da ya faru, kuma ya yi azama ya taho domin ɗaukar fansa.

“Da  ya isa Dumburum, sai ya ji an ce Dangote ya yi shiri zai zo ya yaƙe shi, daga nan ne ya yanke shawara, ya yi musu kwanton ɓauna,  ya samu sa’ar kashe Dangote da yaransa Lamo na Balewa da Usman Yalo.”

Wakikinmu ya gano cewa,  Dan Karami ya samu raunuka yayin da wasu daga cikin yaransa suka mutu.

Wani labarin da ake yadawa kuma shi ne, a lokacin da Sale, yaron Dangote ya bi sawun tumakinsa, sai yaran Dan Karami suka kashe shi da wasu da suka rakoshi.

To daga nan ne wadanda suka gudu ɗin suka je suka shaida wa Dangote abin da ke faruwa.

Wannan ta sa Dangote shiri na musamman domin ɗaukar fansa, sai dai Dangote ya yi rashin sa’a, Dankarami ya riga ya shirya yaransa, kafin ya ankare an masa kwanton ɓauna aka tura shi barzahu.

Dangote da Dan Karami dai na sheƙe ayarsu ce a iyakar Zamfara da Katsina. Kuma an sha samun labarin sabani a tsakaninsu, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane da dama daga cikin ‘yan kungiyoyin nasu da ke gaba da juna.

Aminiya ta gano cewa duk da cewa Dan Karami na rayuwa a Jihar Zamfara ne, duk lokacin da ya fuskanci matsin lamba daga sojoji ya kan yi hijira zuwa Katsina tare da ‘yan kungiyarsa domin neman mafaka.

Dangote ɗaya ne daga cikin ’yan ta’addar da suka addabi yankin Batsari, wani yanki da ke ɗanɗana kuɗarsa a hannun ’yan bindiga da kuma wani sashe a Jihar Zamfara