Rikicin Zangon Kataf: An bukaci a hukunta Zamani Lekwot
Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeria ta nemi Gwamnatin Tarayya da ta sake duba hukuncin da aka yanke wa Zamani Lekwot da sauran shugabannin Kudancin Kaduna dangane da rawar da suka taka a rikicin Zangon Kataf a shekarar 1992. A cewar majalisar rashin yanke musu hukuncin kisa kamar yadda kwamitin binciken da aka kafa […]
Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeria ta nemi Gwamnatin Tarayya da ta sake duba hukuncin da aka yanke wa Zamani Lekwot da sauran shugabannin Kudancin Kaduna dangane da rawar da suka taka a rikicin Zangon Kataf a shekarar 1992.
A cewar majalisar rashin yanke musu hukuncin kisa kamar yadda kwamitin binciken da aka kafa a wancan lokaci ya nemi a yi shi ya sa ake ci gaba da rikici a yankin.
Sakataren Majalisar a Jihar Kaduna Injiniya Abdulrahman ne ya bayyana matsayin majalisar akan Rikicin Kudancin Kaduna a zantawarsa da manema labarai a ranar Alhamis.
“Akwai matsaloli da ke faruwa a wannan yankin wanda an rasa rayuka da dukiyoyi kuma tun shekarar 1981 ake wannan rikici.
“A shekarar 1987, mun ga abun da ya faru a Zangon Kataf yadda aka karkashe Musulmi aka kone musu dukiyoyi.
“Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin bincike ta kuma binciko wadanda ke da laifi, a kuma zartar masu da hukuncin kisa amma gwamnatin wancan lokaci ta yafe musu.
“Yafiya da aka yi musu ita ce ta janyo mana matsalar da muke ciki a yanzu domin Allah Ya ce. Duk wanda ya kashe idan ya san za’a kashe shi ba zai yi ba”, inji shi.