Rikicn Iraki: Mayaka sun ‘kwace Tikriti’ bayan Mosul

A shekaranjiya Laraba mayakan sa-kai a kasar Iraki sun kwace birnin Tikriti birni na biyu mafi girma da suka kwace  bayan Mosul wanda suka kwace a ranar Talatar da ta gabata, kamar yadda mahukuntan kasar suka bayyana.Tikriti wanda shi ne mahaifar marigayi Shugaba Saddam Hussein yana da nisan kilomita 150 Arewa da birnin Baghdad.Firayi Ministan […]

Rikicn Iraki: Mayaka sun ‘kwace Tikriti’ bayan Mosul
Rikicn Iraki: Mayaka sun ‘kwace Tikriti’ bayan Mosul

A shekaranjiya Laraba mayakan sa-kai a kasar Iraki sun kwace birnin Tikriti birni na biyu mafi girma da suka kwace  bayan Mosul wanda suka kwace a ranar Talatar da ta gabata, kamar yadda mahukuntan kasar suka bayyana.
Tikriti wanda shi ne mahaifar marigayi Shugaba Saddam Hussein yana da nisan kilomita 150 Arewa da birnin Baghdad.
Firayi Ministan Iraki Nouri Maliki ya sha alwashin fafattawa da mujahidin kasar tare da hukunta sojojin kasar da suke gudu, ko suka ki tsayawa su fafata da mayakan sa kan.
Maharan wadanda ’ya’yan kungiyar Islamic State of Irak and the Lebant (ISIS), ana zargi suna da alakada kungiyar Alka’ida.
kungiyar ce ke da iko da yankunan da ke gabashin Syria da yamma da tsakiyar Iraki, kuma masu gwagwarmayar mabiya Sunni ne suka kafa ta.
Rahotanni a shekaranjiya Laraba sun ce ana fafata fada a garin Samarra da ked a nisan kilomita 110 daga birnin Baghdad.
A wani labarin kuma akalla mutum 21 suka rasu, yayin da 45 suka samu raunuka a wani harin kunar bakin wake da aka kai wa wani taron ’yan Shi’a a Baghdad kamar yadda ’yan sanda suka ce.
Kimanin mutum dubu 500 suka gudu daga Mosul bayan da mayakan suka kai hari ga birnin. Kuma babban jami’in ofishin jakadancin Turkiyya a Mosul ya ce kusan ma’aikatan jakadanci 50 ne mayakan suka kama.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya yi gargadin cewa za su mayar da ‘martani mai zafi’ idan aka cutar da ’yan kasarta.
Maharan sun hanzarta yin Kudu inda suka shiga garin Baiji a ranar Talata.
Akwai rahotannin da ke cewa ana fafata fada da daruruwa mayakan da suke kai hari ga jami’an tsaro a kusa da hedkwatar gwamnatin gundumar Salaheddin a cikin tsakiyar birnin.
Wani ganau ya shaida wa BBC cewa ’yan bindiga sun shiga birnin ta wurare hudu, kuma an sanya wa wani caji ofis na ’yan sanda wuta.