Rikita-rikitar siyasar Nijar
A Fabrairun shekara mai zuwa ne ake sa ran gudanar da zabe a Jamhuriyyar Nijar. To, sai dai a wannan karon akwai abubuwa da dama da siyasar kasar take fuskanta da za a iya cewa, ba kasafai ’yan kasar suka saba ganin wannan rikita-rikitar siyasar ba, duk da cewa sun saba ganin sabanin da ake […]
A Fabrairun shekara mai zuwa ne ake sa ran gudanar da zabe a Jamhuriyyar Nijar. To, sai dai a wannan karon akwai abubuwa da dama da siyasar kasar take fuskanta da za a iya cewa, ba kasafai ’yan kasar suka saba ganin wannan rikita-rikitar siyasar ba, duk da cewa sun saba ganin sabanin da ake samu a tsakanin jam’iyya mai mulki da kuma sauran jam’iyyun siyasar da ke adawa.
Ita dai Jam’iyyar PNDS Tarayya, wadda ke mulkin kasar karkashin shugabancin Mahman Issoufou ta sha alwashin sake cinye zaben da za a yi a badi.
Alhaji Garba Tumfafi, daya daga cikin magoya bayan jam’iyyar, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ’yan Nijar mazauna Katsina, ya bayyana dalilinsu na sake cin zabe tun a karon farko, ba tare da an kai zagaye na biyu ba.
Garba Tumfafi ya kawo wasu daga cikin dalilan cewa, “Tunda aka kafa Nijar ba a taba samun Shugaban kasar da ya yi mata aiki a cikin kankanen lokaci irin Mahman Issoufou. Ya gina makarantu tun daga kanana zuwa manya, kuma duk akwai kayan aiki da suka hada da littattafai da sauransu. Wanda a yanzu babu dan makarantar da zai ce yana sayen kayan karatu a duk fadin Nijar. Ya kuma dauko hanyar jirgin kasa tun daga Yamai zuwa Dosso, ya wuce har Gaya da wasu kasashen makwabta. Ga asibitoci dubu da Gwamnatin Tandja ta gina, wadanda aka bar su tamkar kangaye, wannan gwamnati ta wadata su da magani da kayan aiki, ciki har da motocin daukar marasa lafiya.”
Alhaji Tumfafi ya ce, hatta gina hanyoyi wannan gwamnati ba a bar ta a baya ba, saboda ta gina hanya tun daga Gidan Rumji zuwa kounni zuwa Yamai daga Tahoua (Tawa) zuwa kounni. Sannan ta kawata babban birnin kasar, Yamai, inda aka gina hanyoyin bisa gadar sama, wadda a da sai dai su ga irin ta a Najeriya ko wasu kasashe.
Da ya juya a kan dalilin kama shugaban jam’iyyar adawa ta Modern Lumana, Alhaji Hama Amadou da gwamnatin kasar ta yi, wanda ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’ar kasar,Tumfafi ya ce, “Ba gwamnati ce ta kama shi ba, shari’a ce ta kama shi saboda (ana zargin) ya aikata laifi. Kuma in bai aikata laifi ba me ya sa ya gudu ya bar kasar? Kuma shi kadai ne aka tuhuma? Ai har da matarsa, kuma suna nan suna yawo a cikin kasa.”
Wannan kamu da jami’an tsaro suka yi wa babban dan adawa a kasar yana da nasaba da tuhumar da gwamnati ta yi masa cewa, ya zo ko yana zuwa Najeriya tare da wasu ciki har da matarsa suna sayen jariran da suke mayarwa tamkar ’ya’yansu, zargin da Hama da sauran wadanda ake zargin suka musanta, wutar guguwar zargin ce ta sanya shi barin kasar tilas zuwa Faransa, wadda ita ce ta yi wa kasar mulkin mallaka domin samun mafakar siyasa.
Shi kuwa Shugaban Jam’iyyar ta Lumana a Jihar Maradi, Alhaji Lawali Leje cewa ya yi, “Duk duniya ta san babu wani dalilin kama Hama sai siyasa kawai. Wannan ya samo asali ne na janyewa daga cikin jam’iyyun kawance da ke mara wa wannan gwamnati baya.
Hama kowa ya sani mutum ne mai kishin kasa da son ci gabanta da al’ummarta, wanda da zarar ya gano cewa, ba ka da irin wannan ra’ayi, to zai rabu da kai. Haka ta faru tsakaninsa da gwamnati. Hasali ma, sai da suka yi kokarin kwace masa jam’iyyar Allah bai yarda ba.” Shugaban na Lumana, ya ce, wane aiki ne za su yi ikirarin sun yi? “Ai kowa ya san tun lokacin da aka samu ’yanci ake aikin gina kasa, kuma dole ne kowane shugaba ya zo ya yi aikin ciyar da kasa gaba. Kuma mafi yawan ayyukan da suke ikirarin su suka yi a cikin shekara hudu tun kafuwar Nijar ba a yi irinsu ba, shin ina ne suka yi aikin? Duk ayyukan sun zo sun tarar da an yi wasu. Ina ne suka gina sabuwar hanya a duk fadin Nijar? Kawai kame-kame ne suke yi. A yanzu haka dan Nijar ba ya cewa yana cin gajiyar man fetur da ake fitarwa daga kasar. Abin takaici sai mun fita waje muke sayen man da sauki. Wannan shi ne aikin? Ga wuraren sayar da magani nan ko’ina a cikin kasa maimakon a asibiti, ina ci gaba yake? Ga wani misali nan, tun lokacin da aka gama aikin kasuwar Maradi, wane mai rumfa ne aka mayar masa da wadda aka karba, an janye mana tattalin arzikin kasa ana fitarwa waje, shi ne aikin?” inji Shugaba Lawali. Ya ce, tuni suka gano makarkashiyar da gwamnati take yi na yin magudin zabe. Ya ce, ko batun yin rajistar masu zabe da aka gudanar duk dan Nijar ya ga irin abin da ya faru, domin an dauki sunan dan wannan jiha an kai wata jihar, wasu ma haka nan aka rubuta sunayensu ba a san su ba.
“Muna kuma da masaniyar irin yadda ake so a yi amfani da wasu ’yan kasa mazauna wasu kasashen domin yin magudin zabe, to mun ce ba mu yarda ba. Har ma wani ikirari suke yi cewa, tun a zagayen farko za su cinye zaben da sama da kashi 50 cikin 100, wanda muke cewa, ko lokacin Tandja wanda ya yi aikin da duk dan kasa ya yaba, a zagayen farko kashi 36 ya samu, a na biyu ya samu kashi 42 cikin 100.
To a ina ne wannan gwamnati mai cike da rashin adalci za ta samu koda na hudu a zabe? Kuma ai za a yi zaben, Haman da ba su so, shi ne zai cinye zaben, ka ce na gaya maka haka.”
Alhaji Lawali, ya yi kira ga duk ’yan kasar Nijar a ciki da waje da su tsaya a kan lallai sai an yi zabe na gaskiya bisa adalci, kada su yarda da duk wani romon baka na mahukuntan kasar wadanda tuni aka san matsayinsu ga al’ummar kasa.
Shi kuwa Shugaban Jam’iyyar adawa ta MNSD Nasara na Jihar Damagaran, jam’iyyar da sojoji suka yi wa juyin mulki a karkashin Shugabancin Tandja, Abdou Adamou cewa ya yi, a zagaye na farko suna sa ran dan takarar jam’iyyar Alhaji Seini Umarou ne, zai cinye zaben, domin batun jam’iyya mai mulki ta ci zagayen farko bai taso ba. “Irin yadda jama’ar Nijar suka waye a kan harkar dimokuradiyya, amma yanzu kowa ya san tafiyar tsutsa siyasarmu take yi. Gwamnati ta kawo rabe-rabe a harkar dimokuradiyyar Nijar, suna so su yi magudi a zabe, mu kuwa mun ce ba mu yarda ba. Lallai sai an yi zabe na gaskiya, kuma mun san ’yan takararmu na majalisa su 30 za mu samu 27 daga cikinsu, tare da Shugaban kasa Seini Umarou. Amma jam’iyyar gwamnati wai tana cewa, tun a zagayen farko za ta ci zabe, to ta yaya ne za ta ci? Aikin me ta yi a kasa? Kowa ya san irin ayyukan da MNSD ta yi a Nijar tun daga kasa har sama. Kuma muna sane da irin yadda gwamnati take so ta yi sama- da-fadi a zaben, shi ma mun ce ba mu yarda ba, sai an yi gyara a kan rajistar masu zabe saboda ta zo da matsala,” inji Abdou Adamou.
Alhaji Ibrahim Tambari, daya daga cikin ’yan takarar majalisa a Jam’iyyar MNSD daga Damagaram a Jihar Zinder ya ce, a shirye suke su kafa gwamnati a kasar. Ya ce, duk wata barazana ta kawo wani cikas ko magudi a zaben suna shirye su fuskanci hakan. Ya yi kira ga ’yan kasar su fito su zabi wadanda suke so, kuma kada su amince da duk wata murdiyar da jam’iyya mai mulki za ta yi musu.