Rita Dominic ta kafa cibiya don yaki da cutar Ebola

Jarumar fina-finan Turanci ta Najeriya (Nollywood) Rita Dominic ta kafa cibiya don yaki da cutar Ebola.Jarumar ta sanar da kafa cibiyarta mai suna Ebola Containment Trust Fund ne a shafinta na Twitter a ranar Talata, sannan ta danka hakkin kula da ita a hannun Dokta Alero Roberts da Christopher Kolade da Fasto Paul Adefarasin na […]

Rita Dominic ta kafa cibiya don yaki da cutar Ebola
Rita Dominic ta kafa cibiya don yaki da cutar Ebola

Jarumar fina-finan Turanci ta Najeriya (Nollywood) Rita Dominic ta kafa cibiya don yaki da cutar Ebola.
Jarumar ta sanar da kafa cibiyarta mai suna Ebola Containment Trust Fund ne a shafinta na Twitter a ranar Talata, sannan ta danka hakkin kula da ita a hannun Dokta Alero Roberts da Christopher Kolade da Fasto Paul Adefarasin na cocin House on the Rock church da Mista Felid Ohiwerei da kuma Mista Gamaliel Onosode.
Ta bukaci ’yan Najeriya su hada kai don a yaki cutar Ebola.
Ta ce: “Barka da warhaka, a yanzu na kafa wata cibiya mai suna Ebola Containment Trust Fund don yaki cutar Ebola. Don haka ya kamata mu hada kai don mu yaki wannan annobar.”
“Na kuma kafa wannan cibiyar ne don bayar da dama ga wadanda suke so su taimaka don a yaki cutar, ina cikin farin ciki a yanzu saboda jama’a sun fara taimakawa.”
Ta ce cibiyar za ta hada kai da gwamnati da kuma jami’an lafiya don ganin an kawo karshen cutar Ebola a Najeriya da ma duniya gaba daya.
Ta ce yanzu haka cibiyar tana yunkurin fito da shafin intanet don wayar da kan jama’a game da cutar, sannan za ta samar da lambobin ko-ta-kwana da za a rika kira.