Robert Mugabe ya yi murabus
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi murabus daga Shugabancin kasar. Shugaban kasar dai ya yi murabus ne bayan jam’iyyarsa mai mulki ta fara shirye-shiryen tsige shi daga mulkin kasar, bayan rundunar sojin kasar ta masa daurin talala na kwanaki. Shi dai Mugabe ya kwashe shekara 37 yana mulkin kasar. Wanda hakan ya nuna cewa […]
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi murabus daga Shugabancin kasar.
Shugaban kasar dai ya yi murabus ne bayan jam’iyyarsa mai mulki ta fara shirye-shiryen tsige shi daga mulkin kasar, bayan rundunar sojin kasar ta masa daurin talala na kwanaki.
Shi dai Mugabe ya kwashe shekara 37 yana mulkin kasar. Wanda hakan ya nuna cewa shi kadai ne shugaban kasar da mutanen kasar suka sani tun samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
A ‘yan kwanakin nan ne kasar ta shiga cikin rudani da rashin tabbas, bayan Mugabe ya tsige mataimakinsa, a wani shiri da masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum suke ganin ya yi ne domin ya maye gurbinsa da matarsa Grace Mugabe.
Tsige mataimakin ke da wuya, sai rundunar sojin kasar ta fitar da sanarwar cewa za ta shiga Tsakani. Sannan daga baya ta yi wa shugaban kasar daurin talala na kwanaki, duk da cewa rundunar ta musanta cewa ta yi juyin mulki.
A makon da ta gabata, an ruwaito cewa ana taron tattaunawa a birnin Harare, amma kuma sai Mugabe ya ce shi fa lallai shi ne halasteccen shugaban Zimbabwe.
Daga nan sai jam’iyyarsa mai mulki ta sanar da cewa ta ba shi zuwa daren jiya domin ya sauka cikin mutunci, ko kuma su je majalisar kasar, inda suke da mafi rinjaye su tsige.
Yanzu haka dai mutanen kasar suna ta murna a titunan kasar domin nuna jin dadinsu bisa yadda Mugabe ya yi murabus.