Roberto Carlos ya zama kocin kulob din Dynamos na Indiya

Tsohon dan kwallon Brazil da kuklob din Real Madrid na Sifen Roberto Carlos ya zama kocin kulob din Delhi Dynamos da ke Indiya, kamar yadda kulob din ya bayar da sanarwar haka a ranar Lahadin da ta gabata. “Muna sanar da duniya daga yau Roberto Carlos ya zama manaja a kulob din Delhi Dynamos da […]

Roberto Carlos ya zama kocin kulob din Dynamos na Indiya
Roberto Carlos ya zama kocin kulob din Dynamos na Indiya

Tsohon dan kwallon Brazil da kuklob din Real Madrid na Sifen Roberto Carlos ya zama kocin kulob din Delhi Dynamos da ke Indiya, kamar yadda kulob din ya bayar da sanarwar haka a ranar Lahadin da ta gabata.

“Muna sanar da duniya daga yau Roberto Carlos ya zama manaja a kulob din Delhi Dynamos da ke wasa a gasar rukuni-rukuni na Indiya” a wata sanarwa da kulob din ya fitar a shafin abota na facebook.
Gasar rukuni-rukuni na Indiya dai tana gudana ne a tsakanin 3 ga watan Oktoba zuwa 20 ga Disamban kowace shekara. Kulob din Dynamos dai bai tabuka abin a-zo-a-gani a kakar wasan da ta wuce ba, al’amarin da ya sa shi yanke shawarar dauko Roberto Carlos don ya taimaka.
Roberto Carlos, dan kimanin shekara 42, ya taba lashewa kasar haihuwarsa Brazil kofin kwallon kafa na duniya a shekartar 2002 kuma yana daga cikin ’yan kwallon da suka sake buga wa kasar gasar cin kofin duniya a 1998. Ya taba yin koci a kulob din Turkiyya mai suna Sibaspor da kuma na Akhaiisar Beledibespor.
Roberto Carlos yana daga cikin ’yan kwallon da suka canza sheka zuwa Indiya don su farfado da martabar kwallo a kasar. Tsofaffin ’yan kwallon da tuni suka koma Indiya sun hada da dan asalin Faransa Nicolas Anelka da Dabid Trezeguet da kuma dan Italiya Alesandro Del Piero.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram