Rodri ya lashe kambun Ballon d’Or na 2024

Rodri ya doke Vinicius da Bellingham wajen lashe kyautar gwarzon Ballon d’Or na bana.

Rodri ya lashe kambun Ballon d’Or na 2024

Ɗan wasan tsakiyar Manchester City da Spain, Rodri ya lashe kambun Gwarzon Ɗan Wasan Ƙwallon Ƙafa na Duniya na bana.

Bikin kyautar na bana ya gudana ne a birnin Paris na ƙasar Faransa.

Rodri ya zama ɗan wasan Manchester City na farko a tarihinta da ya taɓa lashe kyautar.

A bara, dan wasan kasar Ajantina, Lionel Messi ne ya lashe kyautar a karo na bakwai.

Messi ne, ya fi kowa tara kambun, inda yake da bakwai, sai Cristiano Ronaldo na Al Nassr da ke biye masa da guda biyar.

Kyautar Ballon d’Or ta bana ta bar baya da ƙura, inda mutane da dama ke ganin ɗan wasan gaban Real Madrid, Vinicius Junior ne ya fi cancanta ya lashe kyautar duba da irin gudunmawar da ya bai wa ƙungiyar wajen lashe gasar zakarun Turai a bana.

Rodri ya doke Vinicius da Bellingham, waɗanda suka ƙare a matsayi na biyu da na uku.

Rodri dai ya lashe gasar Firimiyar Ingila da Manchester City, sannan ya lashe gasar Euro ta bana da Spain.