Rogon Birni.

Wani Bafillace ne da matarsa ba ta da lafiya sai ya kai ta asibiti, aka ba su gado. Da dare ya yi an dauke wutar Nepa sai likitoci suka rarraba kyandir a kowane gado. Da Bafillace ya dawo sai ya ga ko’ina da haske amma gadonsu babu, sai ya tafi wurin likita ya ce: “Likita, […]

Rogon Birni.
Rogon Birni.

Wani Bafillace ne da matarsa ba ta da lafiya sai ya kai ta asibiti, aka ba su gado. Da dare ya yi an dauke wutar Nepa sai likitoci suka rarraba kyandir a kowane gado. Da Bafillace ya dawo sai ya ga ko’ina da haske amma gadonsu babu, sai ya tafi wurin likita ya ce: “Likita, wajenmu ba wuta.” Sai likitan ya ce: “Ka je, an bai wa matarka.” Yana zuwa ya ce da matarsa: “Ina wutar da aka ba ki?” Sai ta ce: “Ni ba su ba ni wuta ba amma sun ba ni rogon birni, da kyar ma na cinye shi.”
Daga Rabilu Abubakar Gombe, 08036597674