Ronaldo ne mafi tasiri a tsakanin ’yan kwallo a Instagram
Ronaldo yana da mabiya miliyan 480 a Instagram.
Cristiano Ronaldo ya sha gaban kowane mutum a duniya wanda a yanzu yake da mafi yawan mabiya a shafin Instagram.
Wannan ya nuna Ronaldo ya sha gaban Lionel Messi da Neymar da Kylian Mbappe a matsayin mutum mafi yawan jama’a da ke bibiyarsu a Instagram.
- A rika tura mata karatu zuwa Saudiyya —Sarkin Musulmi
- An kama mai shekara 84 ya yi wa ’yar shekara 8 fyade
Ya samu karin mabiya sakamakon Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a cikin watan Nuwamba da Katar za ta karbi bakuncinsa a bana.
Kyaftin din kasar Portugal ya samu karin mutane da ke bibiyarsa da kashi 48 cikin 100 tun daga shekarar da ta gabata.
Wani bincike da Nielsen Gracenote ya gudanar ya ce dan wasan na Manchester United kan samu matsakaicin kudi da ya kai Dala miliyan 3.5 (kusan Naira biliyan biyu) a duk sakon da ya rubuta.
Abokin buga kwallon Ronaldo, kuma dan wasan Manchester United, Jadon Sancho ne kan gaba a kasar Ingila, yayin da Gabi ya samu karin mabiya da kashi 5.165 cikin 100.
Nielsen ya auna wannan ci gaba kan ma’aunin da ya tantance yawan magoya baya da karin mabiya da dan wasa ke samu da yadda ake bibiyar sa da kudin da dan kwallo ke samu a duk lokacin da ya wallafa wani abu a Instagram.
An kuma dora ma’aunin a kan ’yan wasan da za su wakilci kasashensu a Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a cikin watan Nuwamba mai zuwa.
Ronaldo yana da mabiya miliyan 480 a Instagram, Kyaftin din AJentina, Messi ne ke biye da shi da mabiya miliyan 360, wanda ya samu karin kashi 38 cikin 100 – yana samun Dala miliyan 2.6 a duk sakon da ya wallafa a kafar sada zumunta ta Instagram.
‘Yan wasan Paris St German da suka hada da Messi da Neymar da Kylian Mbappe ne ke biye da Ronaldo a mataki na biyu da na uku da kuma na hudu.
Sauran ’yan wasa biyu daga PSG kan karbi matsakaicin kudin da ya kai $1m a duk sakon da suka wallafa a Instagram kamar yadda BBC ta ruwaito.
Cikin jerin 10 farko mafiya mabiya a Instagram tsakanin masu taka leda, dan wasan Brazil mai wasa a Real Madrid, Vinicius Junior ne kan gaba.
Ya samu karin tarin mabiya tun daga lokacin da Real ta doke Liverpool ta lashe Gasar Zakarun Turai na 14 jimilla a kakar bara.