Ronaldo ya ci ƙwallo 900 a tarihin tamaula

Ronaldo ya ci gaba da nuna wa duniya cewa har yanzu ludayinsa na kan dawo.

Ronaldo ya ci ƙwallo 900 a tarihin tamaula

Tauraron ɗan ƙwallo ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo, ya jefa ƙwallo ta 900 a tarihin tamaula.

Ɗan wasa ya kafa wannan tarihin ne yayin wakiltar ƙasarsa ta Portugal a wasan UEFA Nations League da ta fafata da Croatia a filin wasa na Estadio da Luz a ranar Alhamis.

Bayan ƙwallon farko da Diego Dalot ya jefa wa Portugal a minti na bakwai da soma wasan, Ronaldo mai shekaru 39 ya bi sahu a minti na 34.

Ƙwallon da Ronaldo ya jefa tun kafin tafiya hutun rabin lokaci, ita ce cikon ta 131 da ya jefa wa ƙasarsa kuma ta 900 a gaba ɗaya tarihinsa na tamaula.

A watan Satumbar bara ne Cristiano Ronaldo ya ci kwallo ta 850 a tarihinsa na ƙwallon ƙafa a wasan da ƙungiyarsa ta Al Nassr ta doke Al-Hazm da ci 5-1 a gasar Saudi Pro League.

Kazalika, a bara ce Cristiano Ronaldo ya ce yana da burin cin ƙwallo dubu dayta kafin ya yi ritaya daga taka leda.

Ya bayyana wannan kudurin ne bayan shugaban ƙungiyar kwallon kafa ta FC Porto Nuno Pinto ya ƙalubalance shi kan hakan.

Ronaldo ya bayyana ƙudirin ne bayan ya ci kwallonsa ta 857 a wasan da kasarsa ta Portugal ta buga da Slovakia inda aka ta shi 3-2 a watan Oktoba na 2023.

Tun a wancan lokacin ake kallon wannan sabon burin da Ronaldo ya bijiro da shi a matsayin wata alama da ke nuna ba lallai ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa a halin yanzu ba.

Rahotanni sun ce Ronaldo ya nuna sha’awarsa ta sake tsawaita kwantiragi da kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya har zuwa 2027.

Wannan na nufin ɗan wasan wanda ya ci kyautar Ballon d’Or sau biyar zai iya halartar wasan Gasar Kofin Duniya ta 2026 wadda Amurka da Canada da Mexico za su karɓi bakunci.

Haka kuma, a makon jiya ne dai Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin samun kusan mabiya sama da miliyan guda duk awa ɗaya a sabon shafinsa na YouTube, wanda ya sanar da buɗewa.

An sha sanya Cristiano Ronaldo a jerin mafi shahara a kafafen sadarwa a duniya, inda rahotanni ke cewa yana samun miliyoyin kuɗin talla, saboda duk abin da ya wallafa yakan samu kulawa daga mabiyansa cikin ƙanƙanin lokaci.

Babu shakka za a ci gaba da sanya Ronaldo a jerin ’yan wasan da ba a yi kamarsu ba, inda ya tauraruwarsa ta haska ƙungiyoyin da ya wakilta musamman Manchester United da Real Madrid da Juventus.

A yanzu duk da ya doshi shekaru 40, babu wata alama ta tsahirtawa da ɗan wasan ke yi, inda yake ci gaba da nuna wa duniya cewa ludayinsa na kan dawo.