Ronaldo ya ci kwallonsa na 500 a Saudiyya

Ya ci kwallonsa na 500 ne a wasan da ya ci kwallaye hudu a fafatawar da Al-Nassr ta lallasa Al-Wehda 4-0 a Gasar Kwararru ta Kasar Saudiyya

Ronaldo ya ci kwallonsa na 500 a Saudiyya

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin zura kwallaye 500 a sabuwar kungiyarsa ta Al-Nassr da ke kasar Saudiyya.

Ronaldo ya zura kwallonsa na 500 ne a wasan da shi kadai ya ci kwallaye hudu a fafatawar da Al-Nassr ta casa kungiyar Al-Wehda 4-0 a Gasar Kwararru ta Kasar Saudiyya ranar Alhamis da dare.

Dan wasan ya zura kwallonsa na 500 a gasar kulob-kulob ne a minti na 21 ma wasan, inda ya yi murna da irin salon da ya saba.

Kwallonsa na 500 shi ne na biyu tun bayan dawowarsa Al-Nassr daga Manchester United; Daga bisani ya kara na 501, 502 da kuma 503 a ragar Al-Wehda.

A ranar Juma’a, 17 ga watan Fabrairu kuma, Al-Nassr za ta fafata da kungiyar Al-Taawoun a Gasar Zakarun Saudiyya da ke gudana.

Kawo yanzu Ronaldo dan kasar Portugal na da kwallaye 503 da ya ci a kungiyoyi biyar da ya taka wa leda a gasar kulob-kulob.

Ya ci 311 a zamansa a Real Madrid, 103 a lokuta daban-daban a Manchester United, 81 a kungiyar Juventus, uku a Sporting, sai kuma hudu a sabuwar kungiyarsa ta Al-Nassr.

A ranar Juma’a, 17 ga watan Fabrairu da muke ciki kuma Al-Nassr za ta fafata da kungiyar Al-Taawoun a Gasar Zakarun Saudiyya da ke gudana.