Ronaldo ya koma kungiyar Al Nassr ta Saudiyya
Wata majiya ta ce zai karbi albashi Fam miliyan 175 a shekara
Fitaccen dan wasan kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya rattaba hannu kan yarjejeniyar komawa buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr da ke kasar Saudiyya.
Kafar labaran wasanni ta Sky sports ta ce dan wasan ya sanya hannu ne a kan yarjejeniyar shekara biyu a kungiyar da ke birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
- Karin albashi: Gwamnati ta lashe amanta
- Mun kashe ’yan bindiga 54, mun cafke masu fyade 266 a Katsina —’Yan sanda
Wata majiya ta ce zai karbi albashin Fam miliyan 175 a shekara a yayin da kafar Marca ta ruwaito cewar yarjejeniyar ta shekara bakwai ce — zai yi wasa na shekara biyu da rabi sannan ya zama jakada.
Ana hasashen aikinsa a matsayin jakada ya kunshi taimaka wa Saudiyya karbar bakuncin Gasar Kofin Duniya na 2030 da hadin gwiwar kasashen Masar da Girka.
Kafar Al-Ekhbariya ta Saudiyya ta ce a watan Janairu Ronaldo zai fara murza leda a sabuwar kungiyar tasa.
Majiyoyin cikin gida a Al Nassr sun shaida wa kafar CBS cewa a ranar Juma’a da wasan ya rattaba hannu a kan yarjejeniyarsa da kungiyar.
Majiyar ta ce sai da dan wasan mai shekaru 37 ya yi gwajin lafiya na farko gabanin sanya hannu kan takardar yarjejeniyar, kuma a mako mai zuwa zai yi gwaji na biyu.
Dan wasan zai fara wasa a kungiyar Al Nassr ne wata biyu bayan sun yi baram-baram da kungiyarsa ta Manchester United da ke kasar Birtaniya.
Ana ganin komawar Cristiano Ronaldo Saudiyya da murza leda ya kawo karshen tashe sa a harkar tamola, amma kuma zai samu albashi mai tsoka.
Kawo yanzu dai Al Nassr da Ronaldo ba su yi tsokaci kan lamarin ba, ballantana su yi karin haske.
Amma a watan Nuwamba dan wasan ya ce ya ki amsa tayin Dala biliyan 305 daga wata kungiyar kwallon kafa a Saudiyya.
Tun bayan raba gari tsakanin Cristiano Ronaldo da Manchester United dai Al Nassr ta bayyana shirinta na daukar sa.