Ronaldo zai koma PSG
Rahotannin da ke fitowa daga Sifen sun nuna shahararren dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo ya fara yunkurin barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana. Hasalima rahoton ya nuna dan kwallon ya fara yunkurin gabatar da bukatarsa ta barin kulob din ne idan aka kammala kakar wasa ta bana.Rahoton ya ce an bankado […]
Rahotannin da ke fitowa daga Sifen sun nuna shahararren dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo ya fara yunkurin barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana. Hasalima rahoton ya nuna dan kwallon ya fara yunkurin gabatar da bukatarsa ta barin kulob din ne idan aka kammala kakar wasa ta bana.
Rahoton ya ce an bankado ganawar sirrin da Ronaldo ya yi ne da shugaban kulob din PSG Naseer Al-Khelaifi a Faransa jim kadan bayan an tashi wasan da Real Madrid ta lallasa kulob din Wolfsburg na Jamus da ci 3-0 a gasar zakarun kulob na Turai a makon jiya.
An ce wannan ita ce ganawa karo na biyar da dan kwallon ya yi da shugaban PSG a lokuta daban-daban da hakan ta nuna yiwuwar canja shekar Ronaldo zuwa Faransa a karshen kakar wasa ta bana.
Kamar yadda wata mujalla da ake wallafawa a Faransa ta nuna, Ronaldo ya gama da shugaban kulob din PSG ne a wani kasaitaccen Otel da ke Faransa a asirce don haka kafofin yada labarai suka rika yada jita-jitar cewa dan kwallon ya kusa barin kulob din Madrid.
Masana harkar kwallo sun yi hasashen dan kwallon zai iya barin kulob din Madrid ganin shekaru sun fara yi masa nisa, inda yanzu haka yake da shekara 31. Tauraruwar Ronaldo na haskakawa a Madrid tun bayan da Koci Zinedine Zidane ya karbi ragamar horarwa a kulob din.