Ronaldo zai zama Jakadan nemar wa Saudiyya damar shirya Gasar Cin Kofin Duniya na 2030

Dan wasan zai taimaka wa hankoron Saudiyya na karbar bakuncin gasar

Ronaldo zai zama Jakadan nemar wa Saudiyya damar shirya Gasar Cin Kofin Duniya na 2030

Bayan sanya hannu a kan kwantaraginsa da kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr da ke Saudiyya, Cristiano Ronaldo zai taimaka wa kasar a hankoronta na neman karbar bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a 2030.

Fitaccen dan wasan dai ya kammala kokarin tafiya kungiyar ta Saudiyya ne ranar Juma’a gabanin bude kakar musayar ’yan wasa ta bana a watan Janairu.

Dan wasan dai zai rika karbar Yuro miliyan 173 ne a kowacce shekara, ban da sauran kudadn alawus-alawus da zai rika karba.

An dai fara tattaunawar ce yayin Gasar Cin Kofin Duniyar da aka kammala a kasar Qatar, inda a karon farko zai bar Turai da buga wasan nasa.

Rahotanni sun ce dan wasan zai taimaka wa kasar wajen fafutukarta ta karbar bakuncin gasar a 2030.

Kasar wacce ke yankin Gabas ta Tsakiya dai zai za ta ta fafata da kasashen Masar da Girka wajen neman karbar bakuncin gasar nan da shekaru shida masu zuwa.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu