Rooney ya kafa tarihi a kwallon kafa

dan wasan kwallon kafa dan kasar Ingila, Wayne Rooney, ya kafa tarihin zaman dan wasan kasar da ya fi zurara kwallo a raga, inda ya ci kwallaye 50.Rooney ya ci kwallo ta 50 ne a bugun finareti a wasan da Ingila ta doke Switzerland da ci 2-0 domin nema cancantar shiga gasar Zakarun Turai ta […]

Rooney ya kafa tarihi a kwallon kafa
Rooney ya kafa tarihi a kwallon kafa

dan wasan kwallon kafa dan kasar Ingila, Wayne Rooney, ya kafa tarihin zaman dan wasan kasar da ya fi zurara kwallo a raga, inda ya ci kwallaye 50.
Rooney ya ci kwallo ta 50 ne a bugun finareti a wasan da Ingila ta doke Switzerland da ci 2-0 domin nema cancantar shiga gasar Zakarun Turai ta shekarar 2016.
dan wasan da ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United mai shekara 29 a duniya, ya ce wannan tarihi ne da ya dade yana begensa.
A baya dai, dan wasan Ingila, Sa Bobby Charlton ne ya kafa tarihin zama dan kasar da ya fi zura kwallaye – kuma shekara 45 ya yi babu wanda ya kamo shi.