Rubabbun kaya

Babu wanda ya yi mamakin jin yadda tsofaffin ministoci a gwamnatin Goodluck Jonathan ke ta wage bakunansu,  suna yi wa Gwamnatin Muhammadu Buhari da shi kansa tujara game da binciken badakalar da suka aikata, wacce a halin yanzu ake gudanarwa gadan-gadan, kuma za a gurfanar da wadanda aka samu da hannu dumu-dumu a satar dimbin […]

Rubabbun kaya
Rubabbun kaya

Babu wanda ya yi mamakin jin yadda tsofaffin ministoci a gwamnatin Goodluck Jonathan ke ta wage bakunansu,  suna yi wa Gwamnatin Muhammadu Buhari da shi kansa tujara game da binciken badakalar da suka aikata, wacce a halin yanzu ake gudanarwa gadan-gadan, kuma za a gurfanar da wadanda aka samu da hannu dumu-dumu a satar dimbin dukiyar jama’a a zamaninsu. A cewarsu bi-ta-da-kulli ce kawai ake yi masu, babu wani abin da suka aikata na assha, sai dai kawai ana yi masu zargi ne don a tozarta su, a kuma shafa musu kashin kaji.
Wadannan tsofaffin ministocin, a karkashin tsohon ministan tsare-tsare a gwamnatin Goodluck Jonathan, Dokta Abubakar Olanrewaju Suleiman, sun ce ai idan ba a gode wa Gwamnatin Jonathan ba, ba kuma za a tsittsigale mata ba, ana mata kazafin da ba shi da tushe balle makama. Sun ce ai Jonathan ne ya shimfida manufofin da suka wanzar da  nasarorin da Gwamnatin Shugaba Buhari ke tinkaho da su, cikin ‘yan kwanaki kadan da hawanta mulki, domin kuwa idan ba domin haka ba, babu wani abin da za ta yi gadara da shi. A’a? Ai Dokta Jonathan ba wani galhanga ba ne da zai amince ya yi nika wani can dabam ya kwashe garin. Mahaukacin kare ne ya cije shi da zai yarda ya yi hakilon banza, ya zame kurar da za a  yi ta tika, gardi na karbe kudin? Ai daga jin wannan batu ka san surkulle ne mara kan gado.
Babu wata hujjar da wadannan ministoci za su gabatar da za ta nuna rashin dacewar bayyana zarge-zargen mundahana da ake yi musu a kafafen yada labarai. Ai baicin hukumar talbijin ta NTA ta kasa baki daya da kuma rediyon tarayyar Najeriya, watau FRCN, wadanda suka kasance mallakar gwamnati ne, ai mafi yawa daga kafafen yada labarai mallakar ‘yan  shiyyar Kudu-maso-Kudu ne, saboda haka nan wane dalili ne ya hana su kare danuwansu, Dokta Jonathan idan har da ya yi wata rawar gani, ko ya yi abin yabo, fitsari da kumfa? Ai ko ba komai tsofaffin ministocin Jonathan hamshakan masu kudi ne, wadanda ko a birnin Lantsandan suna iya daukar lauyoyin da suka fi sauran tsada don kare su daga zargin da ake yi musu na cutar talakawa.
Idan kuma har suna ganin barazana ce kawai ake yi masu, wacce ke tsorata su, to suna iya riga Gwamnatin Shugaba Buhari garzayawa kotu, kafin ya dankwafar da su gabanta; ko kuma tun da sun sha bayyanawa a takardun sanarwar da suka yi ta rarrabawa manema labarai cewa su ba su damu da barazanar da ake yi masu game da binciken ba, to shi ke nan, sai su tsumayi sakamakon da zai biyo baya, idan aka baje kundin zargin da ake yi masu gaban alkalan da za su bi bahasin haka a tsanake. Ai ido zai raina fata, idan aka bankado laifuffukan da suka aikata, babu kuma wata hujjar kariya da za su gabatar don kare hukuncin da ya dace da ta’asar da suka tattafka. Idan har da gaske suke yi cewa ana tozarta su a kafafen yada labarai bisa abin da suke da’awar ba su aikata ba, to ai kafafen yada labarai ba za su amince da haka ba, muddin sun gasgata cewa Dokta Jonathan ya shimfida ayyukan alherin da yanzu haka gwamnatin Buhari ke cin gajiyarsu.
Ya kamata tsofaffin ministocin Jonathan su fahimci cewa ba gudu, ba ja da baya game da binciken da Shugaba Buhari ke yi, kuma talakawan Najeriya sun amince da haka, suna kuma ba shi goyon baya dari-bisa-dari domin sun san cewa yin haka shi ne mafi alheri ga kasar da kuma al’ummomin cikinta. ]
‘Yan Najeriya dai ba za su ci gaba da amince wa jami’an gwamnati, marasa imani da tsoron Allah, su ci gaba da dulmuya hannayensu cikin randar dukiyar kasar nan, suna dumbuzo dukiyar da suke wofantarwa ba. Abin ban haushi game da soki-burutsun da wadancan tsofaffin ministocin ke yi game da binciken shi ne rashin kunyarsu ta neman Shugaba Buhari ya wallafa dukkan bayanan da ke kunshe cikin kundayen da aka danka masa sa’ilin da Gwamnatin Jonathan ke barin gado. A’a, idan kai na da tsoka me ya hana su shafa nasu, su ji? Ai su ne ya kamata su yi haka idan da akwai kanshin gaskiya cikin bayanan da suka bayar.
To, amma ai ‘yan Najeriya na sane da irin karairayin da suka shirga sa’ilin da suke kan kujerunsu. Sun ce sun inganta wutar lantarki, sun rage farashin man fetur, sun kyautata sufurin jiragen kasa, sun habaka tattalin arzikin Najeriya fiye da na kowace kasa a Afrika. Amma sai dai ‘yan Najeriya sun san cewa wannan zance ne kawai, babu inda aka yi haka.
Saboda haka nan ana iya cewa shugaban wancan sabuwar kungiyar rubabbun kaya, watau tsoffin ministocin Jonathan, Dokta Suleiman tafiya kawai ya yi bisa kansa, ba bisa kafafuwansa ba, kuma mai yiwuwa a kidimewa ya yi aikin ministan, bai san irin almundahana da wala-walar da ‘yan uwansa suka kada wa ‘yan Najeriya ba, suka yi musu coge, suka ci fare da gau, suka bar su haka nan fankan-fayau, ba ko karfafanfana a aljiffansu. Shi da abokanan cin mushensa sun fara nuna damuwarsu a fili, tun da dai ruwa ya kare wa dan kado, ana ganinsa kuri. Yanzu kashinsu zai bushe da zarar an gurfanar da su inda za a yi musu hukunci daidai da yadda suka kuntata wa jama’arsu.