‘Rubewar albasa ta haddasa tsadarta a Najeriya’
Aliyu Maitasamu Isah shi ne sabon zababben Shugaban Kungiyar Manoman Albasa da Sarrafa ta da Kasuwancinta ta Kasa. Mambobin kungiyar ne suka zabe shi makonni biyu da suka gabata a taron da ya gudana a Ma’aikatar Kasuwanci Ciniki da Masana’antu a Abuja. Sabon Shugaban, dan asalin Karamar Hukumar Binji, Jihar Sakkwato, ya tattauna da Aminiya […]
Aliyu Maitasamu Isah shi ne sabon zababben Shugaban Kungiyar Manoman Albasa da Sarrafa ta da Kasuwancinta ta Kasa.
Mambobin kungiyar ne suka zabe shi makonni biyu da suka gabata a taron da ya gudana a Ma’aikatar Kasuwanci Ciniki da Masana’antu a Abuja.
Sabon Shugaban, dan asalin Karamar Hukumar Binji, Jihar Sakkwato, ya tattauna da Aminiya kan dalilin kafa kungiyar da manufofinta da kuma yadda za a samu wadatar albasa a Najeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Mene ne dalilin kafa wannan kungiyar?
Kowa ya san yanzu akwai matsaloli da ake fuskanta a wannan bangare na kasuwancin albasa da nomanta.
Saboda ya dace a ce an samu wata babbar kungiya, wadda za ta daidaita al’amuran albasa a kasar nan, saboda idan ka duba albasa wata shuka ce wacce babu gidan da ba a amfani da ita, wanda idan manomanta ba su dage sun noma ta yadda yakamata ba, za a samu karancinta fadin kasa.
Mene ne manufofin kungiyar?
Manufofin wannan kungiyar shi ne mu inganta noman albasa da sarrafata da inganta kasuwancinta a Najeriya.
Na farko; muna so mu inganta nomanta sannan mu samu damar da zamu nemawa manomanmu bashi ko tallafi daga gwamnati domin ta hanyar kungiya gwamnatin Tarayya ke bai wa manoma bashi irin su Anchor Borrower Programme da sauransu, manomanmu za su iya samun ingantaccen iri da taki da injin ban ruwa da maganin kwari mai inganci, wannan zai sa su kara inganta nomansu.
Idan suka samu wadannan kayan noma za su samu albarkar noma da amfani mai yawa.
Na biyu: Muna so mu daidaita kasuwancinmu idan ka duba muna kasuwanci ne a gargajiyance.
Muna so manyan-manyan manomanmu da ’yan kasuwa su kafa kamfanoninsu na kansu, inda za su iya amfani da sunan kamfaninsu su samo kudi daga bankuna su kara inganta kasuwacinsu, suna iya amfani da sunan kamfanin su rika fitar da albasa kasashen waje.
Hakan zai sa Najeriya ta kara samun kudin shiga, a haka kasar ma sai ta karu a wannan bangaren noma da kasuwancin albasa.
Na uku: Muna so a shekara ta 2025 zuwa 2026, ya kasance ba mu da matsalar albasa gaba daya kuma muna iya cin nasara ne idan Gwamnatin Tarayya da ta jihohi da kananan hukumomi da wasu ma’aikatu kamar hukumar da ke fitar da kaya kasashen waje da ta bunkasa noman lambu da ta masu kula da malaman noma.
Idan aka samu hadin kai da hukomominKwastam da ta shige da fice ta suka shigo ciki to da yardar Allah daga shekarar 2025 zuwa 2026 za mu samu wadatar albasa, kuma muna fatar zuwa karshen shekarar 2021 farashin albasa zai daidaita, idan har gwamnati ta mai da hankali kan wannan shawarar.
Ya aka yi kuka kafa wannan Kungiyar?
Da ma can muna da kungiyar albasa wanda Sarkin Albasar Mai Alfarma Sarkin Musulmi yake jagoranta wato Alhaji Shehu Mai Damo, wannan shugabancin da yake yi ba wai ya kunshi Najeriya kadai bane har da Afirka, wanda na karbi shugabancin gare shi, duk inda dan albasa yake ya yi masa mubaya’a.
Da muka zo mun tarar da wannan tsarin abin da aka yi an mayar da wannan tsarin a zamanance, ana tafiya sai aka nuna mana idan bamu zo irin wannan ma’aikatar ba ba za a san da kungiyar ba, aka zo aka hada kanmu.
Muka zauna muka fitar da dokoki ako ina a yankunan Najeriya akwai: Yankin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma da Yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da ta Gabas aka hadu aka ce shugabanci ya zo daga Sakkwato sai mataimakin shugaba daga Jihar Kebbi sai aka fitar da Sakatare daga jihar da take ta biyu a noman albasa wato Adamawa.
Ina zargin da ake, cewa wasu ’yan kasuwa ne suka boye albasa, hakan ne yahaddasa tsadarta?
Ko kadan albasa idan ta kawo yanzu ba ta boyuwa, dole a fito da ita.
Albasar damina ba a ajiye ta, duk wanda yake da ita yanzu tattali yake yi ya fito da ita.
Ita kuwa sura ko ganinta ba a yi, idan kuma an ganta tana dubu 80 ko dubu 100.
Albasar rani ita ake boyewa a watan hudu zuwa watan biyar na shekara, kuma duk albasar rani da ka bari ta shekara dole ka fitar da ita, idan ka bari sabuwar albasa ta iske ta za ta karya mata farashi.
A yanzu da ake cewa matasa ba su da aikin yi gwamnati ta bai wa matasa iri da injinan ban ruwa su noma albasa, idan sun noma gwamnati ta zo ta saya kowa ya zo ya saya.
Wane shiri kungiyarku ta yi don wadata Najeriya da albasa?
Yanzu muna ganawa da Babban Bankin Najeriya CBN kuma magana ta yi nisa, kuma sun aminta za su ba manoman albasa bashi, kuma abu ne mai kyau da bankin Najeriya ya dauko na gina tattalin arzikin Najeriya domin mu wadatar da kanmu da albasa, saboda idan matsalar rashin albasa ya ci gaba sai mun shigo da albasa daga kasashen wajen.
Muna kira ga CBN da Gwamnatin Tarayya da Ma’aikatar Gona ta Kasa su waiwayi wannan bangaren na albasa saboda a zo a zauna aji daga gare mu menene matsalar mu.
Idan har babban banki ya iya bamu bashi kaga za mu magance rashin ingantaccen iri da rashin ingantaccen taki. Sai kuma gwamnati ta shigo don ta magance mana matsalar rubewar albasa.
Kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na albasar da muke nomawa tana rubewa, saboda babu wajen ajiya, a gina mana wajen ajiyar albasa kuma ta shigo da kamfanoni ta ba su dama su yi wajen sarrafa albasa.
Mene ne sakonka na karshe?
Muna so mu sanar da gwamnati cewa ana shigo mana da albasa da garinta cikin kasar nan daga waje, muna so a hana.
Ko kuma ta kara kudin shigowa da hodar albasar, ya kasance idan aka fada maka kudin da za ka biya to zai hana ka shigowa da ita.
Dalili kuwa shi ne muna nomata sosai sai ka zo ka saya a wajenmu ko ka noma da kanka, sannan albasar Najeriya ta fi kowacce albasa a duniya yaji.