Rubutu da aikin talabijin duk abu guda ne – Shugabar Alminhaj

Hajiya Rahama Abdulmajid ita ce Shugabar Tashar Talabijin ta Alminhaj da ke watsa shirye-shiryenta bisa tauraron dan’adam na Eutesat. Haka kuma ita ce Shugabar Kungiyar Marubuta mata ta Mace-Mutum. A wannan tattaunawar da ta yi da Aminiya, Rahama ta bayyana dalilanta na yin baloguro daga fagen rubuce-rubucen littattafai zuwa fagen watsa shirye-shiryen Talabijin. Kuma tana […]

Rubutu da aikin talabijin duk abu guda ne – Shugabar Alminhaj

Hajiya Rahama Abdulmajid ita ce Shugabar Tashar Talabijin ta Alminhaj da ke watsa shirye-shiryenta bisa tauraron dan’adam na Eutesat. Haka kuma ita ce Shugabar Kungiyar Marubuta mata ta Mace-Mutum. A wannan tattaunawar da ta yi da Aminiya, Rahama ta bayyana dalilanta na yin baloguro daga fagen rubuce-rubucen littattafai zuwa fagen watsa shirye-shiryen Talabijin. Kuma tana nan a fagen rubutun domin ya riga ya zama jini da tsoka a jikinta. A yi karatu lafiya:

 

Mu fara da jin takaitaccen tarihinki?

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarkatuhu. To a takaice dai ni ce marubuciya Rahama Abdulmajid kamar yadda aka sani. Na yi littattafai da dama kuma kusan a rayuwata baki daya da ayyukan da nake ba su gaza alaka da aikina na zama marubuciya ba. Sannan marubuci na tsintar kansa daga wani waje zuwa wani. Sau tari duk abinda ya shafi harkokin adabi da harkar jarida da sauransu duk suna yi wa marubuci sauki ya sauko daga inda yake zuwa can! To ni ma na samu irin wannan tsallakawar, inda yanzu ni ce shugabar wannan gidan TB na Al-Minhaj.

Wadansu za su yi mamakin irin wannan balaguro daga fagen adabi zuwa watsa shirye-shirye a tashar talabijin. Shin ya aka soma?

To Alhamdulillahi dalilan su na da yawa. Akwai wadanda zaka ka sun zo ne kamar ba-zata, ita dai Alminhaj, tasha ce da aka gina saboda harkokin Musulunci da za su tafi da zamanin da muke ciki. Idan ma ka kula da rubutuna zaka ga ina yawan damuwa da addini a zamanance, yadda rayuwa za ta rika kasancewa, ba kullum ana barinmu a baya ba. Ina da wani take da nake yawan fada cewa ‘mu bar jiya ta huta, haka nan ya isa’ to wannan sai ya zama kamar sara akan gaba, da wannan tasha ta Alminjah wacce ta ke kan tauraron Dan’Adam wato Eutelsat 16 ko Arabsat ta zo, sai ya zama dama ina da rajin zuwanta ko makamanciyarta. Da farko ba aikin in shugabance ta ba ne gaskiya ko in zama ma’aikaciyarta ba. Domin an kirani ne in zo in bada gudumowa a fanni na. Amma cikin ikon Allah yanayin maida hankali akan aikin sai ya ja hankalin mahukuntan, kasancewar akwai wadanda ayyukan nasu sun fi nawa yawa, amma sai a rika jira wani bai karaso ba, amma ni a kullum za a sameni na iso ina jira. Sannan kuma ina iya sanya baki cikin ayyukan nasu, to wannan dalili da kuma sanin da aka yi min na son bada gudumawa a fannin ci-gaban addini sai mahukuntan wannan tasha sun ka ga cewa zan iya zama wakiliyar musulmai a wannan tasha. Wannan shi ne abinda ya faru.

Kin yi maganar tafiyar da mulunci a zamanance. Ya tsarin shirye-shiryen wannan tasha su ke?

Wato babban abinda ya bambanta Alminhaj da saura shine, sau da yawa idan aka ce tashar musulunci wasu na jira su ji wa’azi, kiran sallah da sauransu. Wannnan na farko kenan. Na biyu kuma wasu kan jira su ji tashar su wanene? Wa take goyan baya wa ta ke suka da sauransu. Domin a yanzu kusan halin da musulmi suka samu kansu kenan, wasu musulman ma sun bar asalin da’awar addinin sun koma su na neman kura-kuran junansu! To inda wannan tasha ta sha bamban kenan, domin ba ta da akida, illa kawai ta na gogayya ne da duk wani musulmi wanda ra’ayinsa musuluncin nan ya zama daya.

Wanda bai ganin mai furta kalmar La’ilaha’illah a matsayin kafiri don akidarsu ba daya ba! To duk mai irin wannan ra’ayin, tashar Alminhaj na maraba da shi. Sannan mun fadada tunaninmu wajen shigar da abubuwan da suka shafi shakatawa, a wannan tashar ce za ka ga ana tattaunawa akan adabi, domin muna da wani shiri mai taken ‘bitar adabi’ wanda yake janyo marubuta da ‘yan fim da mawaka a maimakon kore su, sai ayi kokarin gano wace gudumawa su ke iya baiwa musulunci? Saboda mun kula dukkansu akwai gudumawar da za su iya badawa, kuma idan ka ba su wannan dama za su iya isar da sakon cikin kiftawa daya, wadda kila wani mai wa’azin ya dauki awa guda! Sannan muna da tsare-tsare na shigo da wadanda su ka hada kai don cimma wata manufa, akwai wani shiri mai suna ‘Wa’atasimu’ wato ta yadda musulmi za su hade su zama tamkar tsintsiya. Shi wannan shiri ya na duba dalilan da suke jawo sabani a tsakanin musulmai da kuma hanyoyin warware su. Wannan shiri ya na ma cikin manyan dalilan kafuwar wannan tasha. Akwai kuma wani shiri ‘Usuwatun hasana’ maimakon tilastawa mutane ko wajabta mu su cewa dole su yi addini a salo kaza, koda kuwa kai ba zaka iya ba, to shi wannan shiri ya na tattaro halayen da idan musulmi a wannan zamanin ya na yi ba zai samu wata wahala ko ya zama dan ta’adda ba. Sannan mu na da shirye-shiryen yara cikin salon yadda ake ba yara labarai kamar tatsuniyoyi da sauransu, amma ba labaran kanzon kurege ba, kamar tarihin Annabawa da daulolin musulunci za a tsara cikin sigar yara ana ba su cikin nishadi. Baya ga wadannan akwai kuma wazozin manyan malamanmu a fannoni daban-daban. Kamar akwai wani shiri da muke ce wa ‘Jami’ar Manzo’ akwai kuma ‘Magada Annabawa’ da sauransu.

Kenan wannan tasha ba ta da bambancin akida. Izala da Tijjanniyya da Kadiriyya da Shi’a duka nata ne?

E lallai haka ne.

Wannan na nuna cewa za a iya ganin ko wane malami na wadannan kungiyoyi a tashar?

Sosai ma kuwa, sai dai abinda zai sa ba a ga wani malamin ba kila ko saboda ya na da alami da zagi ko sukar wani bangare! Idan kuma ya zama haka to ba a nuna shi ba. Amma dukkan malamin da aka san bai da halayyar aibanta wasu, to wannan tasha ta na maraba da shi ko daga wace akida yake. 

Baya ga harshen hausa, kuna da tunanin kara wasu harsunan anan gaba?

Muna da tunanin anan gaba tashar Alminhaj za ta iya karade dukkan manyan harsunan Najeriya. Sannan anan kusa za mu fara shirye-shirye da harshen turanci, duk dai a yunkurin wannan tasha na koyar da al’ummar musulmi kyawawan dabi’u da hadin kai da zaman lafiya da sauransu.

Kasancewarki mace, kila wasu su yi tunanin mata ne za su fi bada gudumawa wajen gabatar da wa’azozi a wannan tasha. Ko haka ne?

A’a gaskiya ba haka ba ne! Ayyukan Alminhaj ba ayyuka ne na son kai ko son zuciya ba. Aiki ne na waye ya dace, waye zai iya. Saboda ba mu na so ne mu rika abubuwa bisa kuskure ba. Dukkan abubuwan da suka shafi mata, mata ne za su yi. Misali mu na da wani shiri ‘Zababbun Mata’ to don gabatar da wannan sai mu ka gayyato mata wajen isar da sakon. Amma idan maganar karatun Alkur’ani da kira’o’insa ka ga wannan aikin maza ne bai dace mace ta yi wannan ba. Don haka wannan tasha ta Alminhaj ta kowa ce sannan ta dukkan iyali ce. 

Rahama ke ce shugabar wannan tasha, haka kuma shugabar kungiyar adabi ta Mace-Mutum. Shin ta ya ya kike tunanin tafiyar da wadannan ayyuka  a lokaci guda?

Wato ai rubutu halitta ce mai zaman kanta. Rai ne da shi da mutuwa, ana haihuwarsa ne a lokacin da aka haifi mai shi. Sannan kuma yana mutuwa ne a lokacin mai shi ya mutu. Kuma zan ma iya cewa harkar adabin ce ta kawo ni wannan matsayi, don haka harkar rubutu ba mutuwa zata yi a tattare da ni ba! Sannan akwai wani abu anan da ya kamata a gane, idan marubuci ya tashi daga rubutun littafi ya koma rubutun fim, har yanzu marubuci ne. Haka kuma idan marubuci ya koma harkar rediyo ko talabijin har yanzu marubuci ne domin sai ya rubuta sannan zai karanta. Don haka dai fage ne mai fadin gaske, ai ko kafin a shigo nan na dade ban rubuta littafi ba, saboda na shiga cikin harkokin rubuta labaran fim da jaridu da sauransu. To a takaice rubutu jini ne da tsoka a jikina ba zan daina shi ba.

Kila masu bibiyar littafanki su yi tsammanin ko kin yi bankwana da rubuta littafi…

…A’a, sai dai kawai idan wahayin bai zo ba. 

Ya za ki kwatanta yanayin isar da sako tsakanin adabi da kuma shirye-shiryen talabijin?

A wajenmu dukkansu suna karkashin adabi ne, ma’ana guda mu ke ba su. Yadda muke kirkirar labari mu mayar da shi mai dadi ga jama’a, anan ma talabijin manufar kenan. Sannan kuma wani kari akan fifikon talabijin shine, mintunan da mutum zai dauka kafin ya karanta shafi guda na littafi kila mai kallo ya ga wannan abin cikin dakika biyar. Ka ga kenan wannan ya fi saurin isar da sako, sannan kuma idan ka ajiye masu karatun littafi 10, to ka samu talabijin 10 kenan, domin kowa da yadda zai saka hotan a zuciyarsa, amma idan ka ajiye mutum 100 a gaban talabijin, dukkan su hota daya suke kallo. Ka ga akwai bambanci.

A matsayinki na mace kuma shugabar wannan tasha, wane kalubale kike fuskanta?

To gaskiya mafi yawa a cikin al’adunmu, wasu mutane su na ganin shugabanci mai dace da mace ba. Duk da dai akwai fahimtoci daban-daban akan wannan babin, cewa wanne ne mace za ta yi wanne ne ba za ta yi ba! Amma mu Alhamdulillahi wadannan matsaloli ba su shafe mu ba. Me yasa nace haka? Shine mu ma’aikatan Alminhaj muna aiki ne a matsayin ‘yan uwa, misali ni a matsayina na shugaba idan akawu bai samu zuwa ba ni zan masa aikinsa, idan mai shara bai samu zuwa ba sai in yi sharar! To haka mu ke a nan gidan. Abinda kawai mutum bai kware ba ne zai jira wanda ya kware ya zo. To da wannan zan iya ce maka ba ni da wani kalubale.

Wasu za su so jin ko harsuna nawa ki ke ji?

Dariya… to har ma sun fara cakude mun! Ka ga ni dai bahaushiya ce, sannan an haife ni cikin yarbawa, har ma akwai lokacin da na so fin jin yarbanci akan hausar. Sannan kuma harshen turanci wanda muka je makaranta da shi. Sannan sai kuma karatun addini wadda da ma shine tafarkin da aka doramu tun farko, har zuwa lokacin da na yi digira a kasar larabawa na karanci harkokin addini. To a takaice dai ina jin yaruka hudu kenan Alhamdulillahi.