Rubutu da marubuta da ci gaban kasa (1)
Harshe kamar yadda aka sani, shi ne sinadarin sarrafawa da kuma aiwatar da duk wani tunani na kowace irin al’umma. Shi ne ke kasancewa na’aurar gudanar da lamurran da suka shafi al’adu da adabi da ma duk wani ilimi na rayuwar dan Adam, a ka ne ko kuma a rubuce. kila wannan dama ce ta […]
Harshe kamar yadda aka sani, shi ne sinadarin sarrafawa da kuma aiwatar da duk wani tunani na kowace irin al’umma. Shi ne ke kasancewa na’aurar gudanar da lamurran da suka shafi al’adu da adabi da ma duk wani ilimi na rayuwar dan Adam, a ka ne ko kuma a rubuce. kila wannan dama ce ta sa ake ba harshe muhammanci, ta yadda wadanda ba su da shi sukan kasance nakasassu, wadanda kuma suke amfani da wani abu makamancinsa, ake musu kallon wadanda ba su cika ba a matasayin mutane a cikin al’umma. A nan ina magana ne kan bebaye ko kuma masu kama da su da kuma masu amfani da fito a matsayin hanyar sadarwa a tsakanin mutane, misali al’ummar Mazatec da ke kasar Medico; haka wannan yanayi yake ko a cikin rubutaccen harshe.
Ke nan duk wadanda ke da hanyar rubuta harshensu, ana yi musu kallon wadanda suka ci gaba, suka fi sauran al’ummomi na duniya wayewar kai da sanin abin da duniya take ciki. Wannan shi ne fasali na farko da aka fara amfani da shi wajen gane bambancin da ke tsakanin Turawa da bakaken fatar Afirka, dab da za a hau dokin mulkin mallaka. Rubutu, ko kuma in ce harshe a takarda shi ne ya sanya wa Turawa ji da kai da kuma tokabo, har suke ganin cewa ba wata hujja da bakaken fatar Afirka za su kyamace su dangane da zuwansu nahiyar a madadin ’yan jari hujjar wancan lokaci, wai don suna da rubutaccen harshe.
Ba sai an fada ba, harshe a magance da kuma rubuce ya samar da wani wagegen gibi tsakanin Turawa da mutanen Afirka, domin kuwa koda suka shigo da alburusai da bindigogi, suka yi amfani da su wajen cin wannan nahiya, daga cikin rubutaccen harshe aka samo tunanin yin haka ba daga wata dabara ta daban ba.
Saboda haka ne ya sa wasu masana da dama irin su Jahn ke bayanin cewa, ai ko da Turawa suka zo Afirka sun iske mu da wayewar kanmu da tunaninmu da kuma ci gaban zamani irin namu, Turawa ba su ne ginshikan ci gabanmu ba. Wani masanin dan rajin wayewar kan Afirka Rodney ya kara jaddada haka ta hanyar cewa ai zuwan Turawan ma ya dakushe ci gaban Afirka da al’ummarta ne a maimakon ya taimaka wajen ciyar da Nahiyar Afirka gaba. Ya kara da cewa ko kafin zuwan Turawa akwai wasu al’ummomi da suke da harshensu a rubuce, akwai kuma wadanda ke da hanyar sadarwa ta gargajiya, irin ’yan ma’abba da kuma kida da ganguna ko makamantan haka, ke nan Afirka wayayya ce, ko kafin zuwan Turawa.
Haka bincike da dama da aka yi kan yanayin mulkin mallaka a Nahiyar Afirka ya kara tabbatar da hasashen wasu masanan Afirka, sun yi nuni da cewa ba abin da mulkin mallaka ya mayar da hankali irin sanya mutunen Afirka su rika tunani da rubutu a cikin harshen da ba nasu ba, a cikin harshen da zai sanya Bature ya rika ci gaba da mulkin bakaken fata ko da kuwa bayan ya nade tabarmarsa ta mulkin danniya da babakere da tsawon shekaru.
Idan aka natsu da kyau aka yi nazari za a ga wannan lamari shi ne a halin yanzu ke faruwa a yawancin kasashen da ake yi wa lakabi da masu tasowa ko kuma wadanda ba su ci gaba ba, ba wai a Nahiyar Afirka kadai ba, har da sassan duniya da makircin mulkin danniya da mallaka ya shiga cikinsu ya yi kaka-gida. Shi ya sa yau kasar Ingila da masu magana da rubutu da harshen Ingilishi a matsayin harshen uwa a cikin kasar Ingila ba su wuce ka kwana ka kirge su ba, amma kuma masu magana da Ingilishi a duniya sun fi kowa yawa a doron kasa, wanda ya sa ake wa harshen lakabi da harshen duniya, ko kuma harshen danniya!
Ana fadin haka ne saboda irin yadda tunani da Ingilishi da rubutu da Ingilishi yake nakasa kowace al’umma da ta ba wannan harshe muhimmanci. Ba yadda za a yi al’umma ta ginu ta kuma ci gaba ba tare da kare harshenta da kuma rubuce-rubucenta ba. Duk irin yadda mutum zai yi ya ciyar da kasarsa gaba ta hanyar amfani da ilimi da ke cikin littafin da ba a harshensa yake ba, zai kasance cikin matsala da kuma kunci, domin zai zamanto mai yaki da tunani iri biyu, na baki da kuma nasa na gida, wannan na daga cikin abubuwan da suka cunkushe harkar iliminmu da kuma targaden da ilimin yake fama da shi a yau.
Wannan abu da muke fama da shi yau, shi ne kuma Turawa suka yi fama da shi a zamanin da Larabci yake tashe a doron kasa, wato daidai zamanin da Larabcin yake cikin ganiyarsa. Kusan duk wani ilimi na kimiyya ko fasaha ko kuma na ci gaban al’umma a Larabce yake, kuma dole ta sa Turawa suka kama hanyar nakaltar Larabci don cin moriyar ilimin da ke kimshe a cikin littattafan Larabawa da ke mulkin duniya a wancan lokaci. Daga baya ne Turawa suka fahimci cewa ai yawancin ilimin da Larabawa ke takama da shi su ma sun kwaso wasu ne daga littattafan Girkawa, don haka suka yi watsi da na Larabawa suka koma wa na ainihin, ta haka ne mallakar da Larabawa suka yi wa duniya ta subuce ta koma ga Turawa.
Wannan ba wani abu ya nuna mana ba sai gadon gida halal ne ga rago. Ba ta yadda za a kai ga kololuwar ilimi da ci gaba ta amfani da bakon harshe, domin kuwa komai iya nakaltar harshen wasu da aka yi, ba za a taba zama kamar su ba, kuma za a kasance ne a kullum ana magana da su bakin, ba mutanen cikin gida ba, domin kuwa kashi 7 cikin 10 na mutanenmu ba su san da wannan bakon harshen ba, idan kuwa haka ne, to mu da wa muke magana a rubuce-rubucenmu? Shin marubutan baya haka suka yi? Yaya tasirin wannan abu yake ga ci gabanmu da al’ummarmu da kuma kasarmu da nahiyarmu?